Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO, ta kira taron gaggawa wanda zai wakana a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya don tattaunawa kan juyin mulkin Nijar.
Wata sanarwa da mai bai wa Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu shawara kan sha’anin sadarwa Dele Alake ya fitar a ranar Juma’a, ta ce taron zai gudana a ranar Lahadi.
A ranar Laraba 26 ga watan Yuli, sojojin da ke tsaron lafiyar shugaban Nijar Mohamed Bazoum suka ayyana karbe ragamar mulkin kasar.
Tuni dakarun suka ayyana Janar Abdouramane Tchiani a matsayin jagoransu wanda shi zai shugabancin kasar.
A matsayinsa na shugaban kungiyar ta ECOWAS/CEDEAO, tun a ranar juyin mulkin, Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da juyin mulkin da sojojin suka ce sun yi.
Ya kuma tura wata tawaga karkashin Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon da ta shiga tsakani.
Kaasahen duniya da dama ciki har da Amurka da Faransa sun yi Allah wadai da juyin mulkin.
Dandalin Mu Tattauna