Yajin aikin da kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta fara a daren jiya litinin ya gurgunta harkokin karatu a makarantun gwamnati na jihar Kano. Makarantun sakandare dana kwalejojin ilimi mai zurfi da kuma Jami’o’i mallakar gwamnatin jihar da na tarayya sun kasance a kulle a yau talata.
Yayin da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya roki Majalisar Dokokin kasar ta shafe dokar da ta bada damar gudanar da zabukan gwamnoni na bai daya a Najeriya, yanzu haka masana dokoki sun fayyace hanyoyin da majalisar ka iya bi domin cimma nasara.
Al’amura sun tsaya cik a majalisun dokokin jihohi 36 na Najeriya tun bayan da ‘yayan kungiyar ma’aikatan Majalisun suka tsunduma yajin aiki a shekaranjiya Litinin. Sai dai masu sharhi na cewa yajin aikin ba shine mafita ba.
Kungiyar, mai suna WANDA Organization mai rajin bunkasa ilimin 'ya 'ya mata akan nazarin kimiyyar sarrafa abinci da samar da shi, ta dauki nauyin karatun dalibai 30 dake karatu a Jami’ar Bayero Kano wadanda ke nazari a fannin kimiyyar sarrafa abinci da dangoginsa.
Tun a farkon shekara ta 2022 ne gwamnatin Najeriya ta amince tare da ba da kwangilar gina layin dogo daga Dutse zuwa Kano da kuma Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar, da nufin habaka harkokin sufuri da na hada-hadar kasuwanci a tsakanin Najeriya da Nijar.
Yayin da aka shiga mako na 2 da barkewar sabon fada tsakanin Isra’ila da Hamas, Zauren Malaman Addinin Musulunci na Najeriya ya bayyana rashin jin dadi kan abubuwan dake faruwa a can, a hannu guda kuma masana sun ce rashin mutunta kudurorin majalisar dinkin duniya suka sa yakin ke ci gaba da faruwa.
Wasu dalilan da suka sa a farkon makon nan kungiyoyin ‘yan kwadago a Najeriya suka janye shirinsu na shiga yajin aikin gama-gari wanda suka so farawa daga ranar 3 ga watan Oktoba
Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa dangane da tsadar albarkatun mai biyo bayan cire tallafin gwamnati tun kimanin watanni biyar da suka shude, masu gidajen man a yankin arewacin kasar sunce harkokinsu na fuskantar barazanar durkushewa, amma masana tattalin arziki sun ce akwai mafita.
Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani game da hukuncin babbar kotun tarayya da ya umarci gwamnatin ta biya diyyar naira biliyan 30 ga ‘yan kasuwar da ta rusa wa shaguna da gine gine a gefen babban Masallacin Idi na Kano kimanin watanni uku da su ka gabata.
Yayin da tsadar rayuwa ta hanyar tashin farashin kayayyaki, musamman na masarufi ke karuwa a Najeriya, shugabannin sarautun gargajiya a kasar na ci gaba da rokon hukumomi su kara kaimi wajen daukar matakan da suka dace domin samar da sassauci ga yanayin kuncin rayuwa da talakawa ke ciki.
Bayan hukunci da kotun sauraron kararrakin zabe a jihar Kano ta yanke, inda ta umarci hukumar zaben Najeriya ta bai wa Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC shaidar cin zaben da aka yi a cikin watan Maris da ya gabata, lauyoyin da ke kare jam'iyyar NNPP sun ce za su daukaka kara.
Cikin tsauraran matakan tsaro irin na ba sabun ba, a yau Laraba kotun sauraran kararrakin zabe ta yanke hukunci kan korafin sakamakon zaben gwamnan Kano.
Domin Kari