Jihohi bakwai ne suka fita daga jerin zabukan bai daya a NAJERIYAR biyo bayan shari’un da aka tafka a shekaruun baya dangane da kujerar gwamnonin jihohin game da sakamakon zabe.
Jihar Bayelsa da Kogi da Imo na cikin wadannan jihohi wadanda akayi zaben kujearun gwamnonin su a shekaran jiya Asabar.
Bayan ya jefa kuri’a a garin su na Otuoke dake jihar Bayelsa, tsohon shugaban Najeriya Dr Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana damuwa akan yadda yace rashin zabukan gwamnoni na bai daya ke neman jefa demokaradiyyar Najeriya cikin rudani, yana mai kira ga majalisar dokokin kasar ta shafe wannan tsari daga kundin mulkin tarayya.
Dr Sa’idu Ahmad Dukawa masanin kimiyyar siyasa ne a Jami’ar Bayero Kano, wanda yayi tsokaci akan wannan batu yace “Ana mayr da zabe kamar yaki za’ayi, gwamnatin tarayya na tattara karfinta a jihar da za’ayi zaben, haka ma jam’iyyun siyasa, musamman babbar Jam’iyyar hamayya a kasa tana mayar da karfin ga wannan jiha kwaya daya. A dalilin haka, ana wahalar da kowa dayake da alaka da wannan zaben”.
Baya ga manazarta a fagen kimiyyar siyasa, ‘yan siyasar irin su Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa sun tofa albarkacin bakin su. “Tun tuni ya kamata ace su ‘yan majalisar dokokin na kasa su dauki matakan gyaran kudin tsarin mulkin Najeriya, domin a dai-daita harkin zabe a kasar nan”.
Sai dai masana dokokin kasa irin su Farfesa Nasiru Adamu Aliyu mai lambar kwarewar aikin lauya ta SAN sun fayyace matakan da doka tayi tanadi akan wannan batu. “Kafin a daidaita wannan said ai ‘yan majalisar dokoki na kasa suyi kwaskwarima ga sashi na 180 na kundin tsarin mulkin kasa, su kara cewa, duk wanda akayi shari’a ya hau kujerar gwamnan jiha to zai dora ne akan watanni ko shekarun da wanda kotu ta sauke ya, ma’ana zai kammala wa’adin mutum na farko da kotu ta karba a hannun sa, amma ba ya farad aga farko ba”.
Masu kula harkokin shari’un zabe a Najeriya na hasashen cewa ta yuwu a samu Karin jihohin da ka iya fita daga jerin zabukan gama gari bayan kammala shari’un da ake tafkawa akan wasu daga cikin kujerun gwamnoni game da takaddamar data biyo bayan zaben watan Maris na bana.
Dandalin Mu Tattauna