Kotun sauraron karar zabe a jihar Kano ta ayyana dan takarar jam'iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano na watan Maris din 2023, inda ta soke nasarar da Abba Kabir Yusuf ya samu.
Kotun ta kuma bayar da umarnin a janye takardar shaidar cin zabe da INEC ta mika wa Abba Kabir Yusuf tare da bayar da takardar shaidar cin zabe ga Gawuna.
Jam’iyyar APC ce ta shigar da kara gaban kotun tana kalubalantar nasarar da Jam’iyyar NNPP tayi a zaben da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris na bana.
Tun a jiya Talata ne aka jibge dinbin Jami’an tsaro a muhimman wurare na sassan birnin Kano. Jami’an sun hada da sojoji da ‘yan sanda, da dakarun tsaro na Civil Defense, da kuma Jami’an farin kaya na hukumar DSS.
Tun da almurun jiya ne jami’an suka rinka sintiri a bangarorin birnin na Kano, al’amarin da wasu ke gani wani mataki ne na tabbatar da doka da oda, a gabani da kuma bayan sanar da hukuncin kotun.
A hannu guda kuma, magoya bayan Jami’yyun da ke fafatawa a kotun ne suka yi dafifi a wasu kofofin shiga birnin Kano da kuma wasu muhimman wurare suna dakon yadda zata kasance.
Baya ga haka, galibin makarantun Kano, musamman na sakandare da Firamare sun kasance a kulle, yayin da kalilan din da suka bude domin daukar darasi suka umarci dalibai da su koma gida.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, ba’a bude cibiyoyin hada-hadar kasuwanci, shaguna da kantuna ba a wasu bangarori na Kano, yayin da a gefe guda kuma, babu ababen hawa sosai akan manyan titinan birnin, duka a kokarin kaucewa abin da ka iya faruwa.
Dandalin Mu Tattauna