A kokarinta na kula da rayuwar matasa, a fannin kiwon lafiya da ilimin zamantakewa da kuma dogaro da kai a tsakanin kasashe masu tasowa, hukumar raya kasashe ta Amurka-USAID ta dauki nauyin wani shirin bunkasa rayuwar matasa ‘yan shekaru 15 - 21, musamman wadanda ba sa zuwa makarantun boko.
Rahotanni daga Kano a Najeriya sun ce ayyukan manya da kananan masana’antu a birnin sun tsaya cik sanadiyyar katsewar wutar lantarki da aka fuskanta tsawon sa’o’i da dama a sassan kasar, al’amarin da ya haifar da mummunan koma baya ta fuskar hadahadar tattalin arziki.
Yayin da wasu ‘yan Majalisar Dokokin Najeriya ke rasa kujerun su a zauren kotunan sauraron kararrakin zabe a jihohi dabam daban na kasar, masana kimiyyar siyasa sun bayyana dalilan da ke sa wasu ‘yan siyasar ke faduwa zabe a gaban kotu.
Rikicin cikin gida na Jam’iyyar NNPP na ci gaba da zafafa bayan da uwar Jam’iyyar ta bayyana korar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, mutumin da ya yi mata takarar shugabancin Najeriya a zaben da ya gabata.
‘Yan kasuwar yankin arewacin Najeriya na ci gaba da bayyana zullumi saboda barazanar da dukiyar su ke fuskanta, yayin da iyakokin Najeriya da Nijar ke ci gaba da zama a garkame biyo bayan takunkumin cinikayya da kungiyar ECOWAS karkashin shugaba Tinubu ta sanya akan Jamhuriyar ta Nijar .
Yayin da ake gudanar da gangami da bukukuwa domin fadakar da al’uma game da zagayowar ranar matasa ta duniya, da alama matasan a Najeriya sun fara nuna shakku kan yiwuwar shugabanni ka iya sama musu mafita dangane da kalubalen rayuwa da suke fama dashi.
Yayin da wa’adin rufe rijistar dalibai na bana a Jami’ar Bayero Kano ke cika, kungiyar tsoffin daliban Jami’ar lokacin tana karkashin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, ta shiga tsakani.
Masu ruwa da tsaki a harkar kanana da matsakaitan masana'antu sun gana a Kano domin samo mafita akan matsalolin da suke hana 'yan kasuwa samun tallafi a arewacin Najeriya.
Taron masu ruwa da tsaki kan harkokin bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu ya koka kan yadda mutanen lardin arewacin Najeriya ba sa samun damar cin gajiyar lamani da tallafin da gwamnatin tarayya, bankuna, cibiyoyin raya tattalin arziki kan bayar da nufin ciyar da tattalin arzikin al’uma gaba.
Biyo bayan zanga zangar lumana na rashin jin dadi game da halin kunci da al’umar kasar suka shiga, masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun fara mayar da martani dangane da nasara ko tasirin zanga zanga.
Mako guda bayan kaddamar da majalisar zartarwa a jihar Jigawa ta Najeriya, al’ummar jihar na ci gaba da dakon ji daga gwamnan jihar Malam Umar Namdi game da halin da lalitar jihar ke ciki.
Domin Kari