Kungiyoyin rajin shugabanci na gari a jihar Kano sun yi Allah wadai da kalaman tunzura Jama’a na baya-bayan nan da suka fito daga bakunan shugabannin Jam’iyyun APC da NNPP na jihar ta Kano.
Jama'a da dama a kudu da arewacin Najeriya sun fuskanci matsalar ambaliyar ruwa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da asarar dukiyoyi.
Yau Alhamis aka shiga rana ta biyu da fara sauraron shiri’ar mutumin kasar China nan Mr Frank Geng Quatrong wanda ake tuhuma da kisan gilla ga Ummukulsum Sani Buhari a Kano a ranar 16 ga watan satumba.
Al’umar wadannan yankuna sun ce za su yi amfani da katunansu na zabe wajen neman mafita, suna masu cewa, duk dan siyasar da ya zo neman kuri’unsu, sai ya musu alkawarin sama musu ababen more rayuwa kafin su zabe shi.
‘Yan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakin su dangane da hukuncin Bulala da shara da wata kotun Majistire a Kano ta yankewa wasu matasa wadanda suka amsa laifin batanci ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a kafar sada zumunci ta Tiktok.
Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa, masu sayan amfanin gona a kakar bana, na bin manona har gonakinsu suna cinikayyar kayan abinci da manoman suka samar, inda suke biyan duk abin da suka saya kudi a hannu
Kungiyoyin rajin demokaradiyya da shugabanci na gari a Najeriya da Jam’iyyun hamayya sun bukaci rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano ta sanar da Jama’a halin da ake ciki game da wani dan Jam’iyyar APC da ‘yan sanda suka kama da katunan zabe fiye da dari uku.
A lokuta da dama, rashin irin wannan alaka kan sa a rika tauyewa talakawa hakkokinsu kamar yadda bincike ya nuna.
Mataimakin sifeton ‘yan sandan Najeriya mai kula da shiyya ta daya da ke Kano ya umarci kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano ya gudanar da kwakkwaran bincike game da cin zarafin da shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan Najeriya, Alhassan Ado Doguwa, ya yi wa wakilin jaridar Leadership.
Amfani da kafofin sada zumunta wajen samun ilimi na gari da cusa tarbiyya a tsakanin dalibai a dukkanin matakai, na daga cikin batutuwan da suka mamaye laccar shekara-shekara ta bana da kwalejin Excel a Kano ke shiryawa iyaye, malamai da dalibai da sauran masu ruwa da tsaki.
A hira da Muryar Amurka a Kano, Manjo Almustapha, ya ce kokarin batawa Abacha suna ne ya sa ake ci gaba da alakanta shi da wadancan kudade shekaru 22 bayan rasuwarsa.
Hukumar tabbatar da ingancin kayayyaki ta Najeriya - S.O.N, ta kaddamar da sabon tsarin auna kayayyaki a Kano, da nufin ganin cewa kayayyakin da ake sarrafawa a Najeriya sun karbu a kasuwannin duniya.
Maniyyatan da ba su sami sukunin zuwa aikin hajjin bana ba daga jihar Kano sun fara karbar kudaden su daga hannun hukumar kula da ayyukan hajji ta jihar.
Shugaban bankin raya kasashen Musulmi, wato Islamic Development Bank, Dr. Muhammad Sulaiman Al-Jessar, ya kammala ziyarar aiki ta yini biyu a Najeriya.
Taron ganawa da masu ruwa da tsaki a muhimman bangarori na al’umar jihar Kano a Najeriya da dan takarar shugaban kasar na Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya shiga rana ta uku.
Yanzu haka dai wakilai daga jihohin arewa 19 da na hukumar kula da birnin tarayya Abuja, wakilan bankin duniya da jami’an gwamnatin tarayya sun hallara a nan Kano inda suke tattaunawa tare da mahawara akan daftarin aiwatar da shirin cikin shekaru shida masu zuwa.
Domin Kari