KANO, NIGERIA - Al’amarin na cin zarafin wakilin jaridar Leadership a Kano, Abdullahi Yakubu, a ranar Litinin da ta gabata ya faru ne lokacin da shi wannan dan Majalisa dake wakiltar kananan hukumomin Tudunwada da Doguwa a Majalisar Tarayya, ya kira taron manema labarai domin fadar nasa labarin kan takaddamar da aka ce ta wakana tsakaninsa da ‘dan takarar mataimakin gwamnan Kano a Jam’iyyar su ta APC, Alhaji Murtala Sule Garo, a yayin wani taro nasu a karshen mako, inda har ta kai shi dan majalisar ya raunata Murtalan.
Shi-ma Abdullahi Yakubu, wakilin jaridar Leaship a Kano, ya fuskanci makamancin wannan yanayi na Murtala, koda yake marin shi ta bayan kunnen sa aka yi, sanadiyyar yunkurin bada shawara da ya yi kan wa su kalamai daya ji sun fito daga bakin Alhassan Ado.
Koda yake an ce sun yi abota a can shekarun baya, amma Abdullahi Yakubun ya nemi hakkin cin zarafinsa a kotu, kuma ba tare da bata lokaci ba aka rubuta takardar umarni ga Mataimakin Sifeton ‘yan sanda mai kula da shiyya ta daya ya binciki wannan batu.
SP Abubakar Zayyanu Ambursa, kakakin shiyya ta daya ta rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke Kano, ya tabbatar da samun takardar umarnin daga kotun Majistire dake Gyadi-Gyadi a Kano kuma ya ce tuni Mataimakin Babban Sifeton ‘yan sandan ya mika takardar ga kwamishinan ‘yan sanda na Kano tare da ba shi umarnin gudanar da cikekken bincike game da lamarin.
Ya ce za a mika sakamakon binciken ga kotun bayan kammalawa.
Sai dai kungiyoyin rajin shugabanci na gari da tabbatar da demokaradiyya a Najeriya sun ce akwai bukatar ‘yan sanda su gudanar da sahihin bincike akan wannan batu.
Comrade Abdulrazak Alkali daraktan kungiyar OCCEN masu wayar da kan jama’a kan harkokin demokaradiyya, ya ce akwai bukatar ‘yan sanda su yi abin da ya kamata akan wannan batu, la’akari da muhimmancin rawar da ‘yan jarida ke takawa ga ci gaban demokaradiyya.
A nata bangaren, kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen Jihar Kano ta ce ba zata lamunce da wannan aika-aika akan ‘ya'yan ta ba. Comrade Abba Murtala Sakataren reshen Jihar Kano na kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, ya ce sun kafa kwamiti domin gudanar da kwakkwakwaran bincike kuma za su tabbatar da karewa tare da kwato hakkin ‘dan kungiyarsu.
A wani labarin kuma, wasu matasa sunyi aikin kakkabe kusan dukkanin manyan allunan da ke dauke da hotunan ‘dan takarar gwamnan Kano karkashin inuwar Jam'iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da na mataimakinsa, Murtala Sule Garo. Matasan sun bi manyan titunan birnin Kano da sauran muhimman wurare da aka kafa irin wadannan alluna.
Saurari cikakken rahoton daga Mahmud Ibrahim Kwari: