Ganawar dake zaman dandalin sabunta alkawura ga masu zabe, gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ke jagorantar ta, tun daga ranar asabar da ta gabata bayan da dan takarar na APC ya sauka a birnin Kano, a wani mataki na neman kuri’a, amma ta salon ganawa da shugabannin rukunin al’uma, domin fahimtar dasu manufofin sa.
Shugabannin ‘yan kasuwa da kungiyoyin siyasa da na kwararru a fannoni daban daban na daga cikin rukunin farko da dan takarar shugabancin Najeriyar na APC Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya fara ganawa da su, inda yayi musu alkawura daban-daban, ciki kuwa har da batun farfado da tattalin arzikin arewa, ta hanyar yashe kogin Neja da tabbatar da tashar lantarki ta Mambila da kuma kammala aikin layin dogo daga Lagos zuwa Kano.
A jiya lahadi ma dan takarar na APC ya gana da shugabannin addinai da suka hada dana darikar Qadiriyya da Tijjaniya da Izala da Limaman Masallatan Juma’a na Kano, kana daga bisani ya karkare da karbar bakuncin shugabancin kungiyar CAN ta Kiristocin Najeriya reshen jihar Kano.
Sheikh Muhammad Nasir Adam dake zaman shugaban majalisar limaman masallatan Juma’a na jihar Kano ya shawarci Bola Tinubu ya kaucewa nuna banbanci bayan samun nasara, yana mai horon sa cewa, ya maida hankali wajen samar da ayyuka ga matasa da kuma martaba addinai a yayin shugabanci.
A jawabinsa, ga dinbin shugabannin darikun da limaman masallatan Juma’ar, dan takarar na APC, Bola Tinubu yace, “yayin da nake tsaye a gabanku ina mai ba ku tabbacin cewa, cikin yardar Allah Najeriya zata bunkasa kuma mafarkin mu na samun kasa abar alfahari zai zama gaskiya ta hanyar cika alkawuran da muka dauka”.
Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar dake shugabancin kwamitin yakin neman zabe na Tinubu a jihahi 19 na arewacin Najeriya ya ce manufar wannan ganawar, ita ce samun kusanci da muhimman bangarorin al’umma domin tattauna matsalolin da suka shafi kasa, musamman lardin arewa, gabanin fara gangamin siyasa n agama gari.
A yau litinin ne dai Bola Ahmed Tinubun ke karkare wannan ziyarar bayan ganawa da sarakuna 5 na jihar Kano da marecen jiya da kuma rukunin ‘yan siyasa daban daban a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya.
Saurare rahoton a sauti: