An gudanar da addu'oin neman dauki daga Allah kenan kafin bude bakin Azumin karshe na wannan shekara a masallachin Juma'a na NNPC da ke Kaduna.
A yammacin jiya Laraba ne dai aka sako daliban na kolejin horar da shi'anin gandun daji da ke Afaka a jahar Kaduna i
Al'umomin dake zaune a garuruwan da ke tsakanin Chukun, Udawa, Kuriga da Birnin Gwari sun ce hare-haren'yan-bindiga a yankin ya yi sanadin rashin garuruwan da ba su san adadin su ba.
Kwana guda da sake sace dalibai a jahar Kaduna, gwamnatin jahar ta ce har yanzu ba wani labari game da adadin daliban da aka sace ko kuma inda aka boye su.
A yayin da ake ganin hare-haren 'yan-bindiga sun yi sauki a watan Ramadan, al'umar garuruwan Kuriga da Udawa da kewaye dake karamar hukumar Chukun jahar Kaduna sun ce su hare-haren ma ta'azzara su ka yi a wannan wata na Azumi.
Jami'an tsaro sun yi nasarar ceto 180 daga cikin daliban Kwalejin Gandun Daji da ke Mando, Kaduna wadanda 'yan bindiga su ka yi awon gaba da su, amma saura 30 ba a san inda su ke da kuma halin da su ke ciki ba
Maganar dakatar da almajiranci na ci gaba da daukar hankali a jihar Kaduna, saboda gwamnati ta dage kan cewa, za a kama duk malamin da ya kawo almajirai. jihar.
Hare-haren 'yan-bindiga da masu garkuwa da mutane a yankin Kerawan karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna ya sa mutanen wasu kauyuka kauracewa garuruwan su zuwa garin Birnin Yero domin neman mafaka.
A daidai lokacin da ake fama da matsalar tsaro a wasu yankunan jihar Kaduna, wani abun fashewa ya tarwatse inda ya jikkata yara bakwai a Anguwar Mangwaro da ke karamar hukumar Igabi.
Adadin fulani 'yan gudun hijira daga kudancin Najeriya zuwa jihar Kaduna na kara karuwa, a yayin da shugabannin fulanin ke nuna damuwa game da abin da ka iya biyo baya.
Tun bayan hallaka mutane goma sha tara da 'yan-bindiga su ka yi a garin Kadanya da ke Kutemeshi a Karamar hukumar Birnin Gwari, al'umar garuruwan da ke yankin sun dukufa wajen gudun hijira don tsira da rayukansu.
A karo na biyu an dakatar da taron manema labarai da gamayyar kungiyoyin Arewa (CNG) ta shirya a garin Kaduna, inda aka jibge jami’an tsaro tare da kame wasu shugabannin kungiyar.
Kungiyar Miyetti Allah ta gargadi ‘ya‘yanta da kar su dauki wani matakin ramuwa, game da harin da aka kai kan Fulani a garin Kurmin Bi na karamar hukumar Zangon Kataf.
Lamarin tsaro na ci gaba da tabarbarewa a daidai lokacin da hare-haren ‘yan ta’adda da masu satar mutane domin kudin fansa ke addabar wasu yankuna na jihar Kaduna.
'Yan Najeriya na ci gaba da kokawa game da matsalar tsaro a kasar musamman ma batun harin da 'yan bindiga suka kai kwanan nan a wata makantar kwana da ke garin Kankara a jihar Katsina.
Hadakar kungiyoyi matasa masu zaman kansu a Najeriya sun gudanar da wani taro, akan tabarbarewar tsaro a Arewacin kasar.
Ganin yadda ake alakanta matsalolin tsaro da sace mutane don neman kudin fansa ga Fulani a Najeriya, ya sa kungiyar ci gaban makiyaya da habaka al'adar su ta FUDECO shirya taron bayyana matsayin su game da irin wannan zarge-zarge.
Domin Kari