Sarkin wanda da ma babban manomi ne ya je gona ne a ranar Litinin inda a nan ne 'yan-bindiga su ka sace shi.
Har zuwa cikin daren jiya Litinin dai babu wani labarin inda ‘yan-bindigan suka kai sarkin amma dai mai magana da yawun rundunar 'yan-sandan jihar Kaduna Muhammad Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarain kamar yadda ita ma kungiyar al'umar kudanchin Kaduna ta shedawa mana ta bakin kakakin ta Mr. Luka Biniyet.
Sace sarkin masarautar Jaba, Mr Jonathan Gyet Maude dai ita ce ta biyu cikin wannan wata a jihar Kaduna abin da ya sa wasu masana tsaro ke ganin akwai siyasa cikin lamarin baki daya.
Birgediya General Mohammadu Kabiru Galadanchi mai-ritaya na cikin masu wannan tunani.
Wannan kuma bai hana al'umar kudanchin Kaduna nuna damuwar cewa su wannan matsala ta fi addaba ba. Har ma kakakin kungiyar na cewa maganar sace mu su sarakuna, ba yau farau ba.
Har zuwa lokachin hada wannan rahoto dai gwamnatin jihar Kaduna ba ta fitar da sanarwa game da sace sarkin na Jaba ba.
Amma dai gwamnan jihar Kaduna Malam Nasuru Ahmed El-rufa'i ya shedawa mahalarta wani taron masu ruwa da tsaki cewa, yanzu haka jami'an tsaro na ta fatattakar 'yan-bindiga a dazuzzukan Kaduna, shi ya sa ma gwamnatin ta dage komawa makarantu don kada 'yan-bindigan da ke guduwa daga daji su huce akan makarantun jihar kamar yadda aka yi ta gani a baya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Isah Lawal Ikara: