Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kaduna Da Kungiyar Kwadago Na Shirin Sake Kai Ruwa Rana


Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, Ayuba Wabba yana jawabi a wajen zanga-zangar (Twitter/NLC)
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, Ayuba Wabba yana jawabi a wajen zanga-zangar (Twitter/NLC)

Da alamu dai tsugune ba ta kare ba tsakanin gwamnatin jihar Kaduna dake arewacin Najeriya da kuma kungiyar kwadago game da maganar rage ma'aikatan da ya janyo zanga-zanga da yajin aiki a jihar baki daya.

Kungiyar kwadagon ta sake sanar da sabon shirin shiga yajin aiki ne da kuma zanga-zanga biyo bayan gaza samun maslaha duk da sulhun da gwamnatin tarayya ta yi tsakanin ta da gwamnatin jihar Kaduna.

Da ma dai ministan kwadago da samar da ayyukan yi Sanata Chris Ngige ne ya shiga tsakanin gwamnatin Jihar Kaduna nan da kuma kungiyar kwadago don kawo karshen rashin fahimtar da aka samu a baya.

Sai dai kungiyar kwadagon ta ce gwamnatin Kaduna ba da gaske ta ke ba.

Shugaban kungiyar kwadago reshen jIhar Kaduna Kwamared Ayuba Magaji Suleman bayyanawa Muryar Amurka matakin da kungiyar ta kasa za ta dauka.

"Cikin yarjejeniyar da muka yi, babu cin zarafin wani ma'aikaci don ya shiga yajin aiki, amma bayan haka sai aka fara wulakanta ma'aikatan." In ji Suleman.

Sai dai gwamnatin Jihar Kaduna ta ce kungiyar kwadagon ce ma ta saba ka'ida saboda haka ba za ta lamunci sabon yajin aiki da zanga-zanga ba, inji mai-magana da yawun gwamnan Kaduna, Malam Ibrahim Musa.

"Idan haka ne, shin ya kamata su yanke hukunci? Mutanen nan sun saba karya doka da sunan suna so su bi wa ma'aikata hakkinsu. Za mu bar su da jama'a su yi hukunci, kuma duk mutumin da ya taka doka, gwamnati ba za ta bar shi ba."

Tuni dai wannan sanarwar yajin aiki da zanga-zanga ta jefa al’umar Jihar cikin tunani ganin irin halin da su ka shiga a zanga-zangar baya.

Yanzu dai abun tsayawa a gani shine yadda za a kwaranye tsakanin gwamnatin Kaduna da kuma kungiyar kwadago.

Saurari rahoto cikin sauti daga Isah Lawal Ikara:

Gwamnatin Kaduna Da Kungiyar Kwadago na Shirim Sake Kai Ruwa Rana - 3'28"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00


XS
SM
MD
LG