Tuni dai Jamiyyar APC ta kammala shirye-shiryen karbar gwamna Muhammed Bello Matawalle kamar yadda shugaban kwamitin riko na Jam'iyyar kuma gwamnan Jihar Yobe Malam Mai-Mala Buni ke ta sanarwa.
Sai dai kuma jagororin Jamiyyar APC a jihar ta Zamfara karkashin shugabanchin tsohon gwamnan Jihar Alhaji Abdul'aziz Yari sun ce sauyin shekarar na da alamar tambaya domin ba a bi ka'idojin da ya kamata a bi ba.
"Muna nan muna tattaunawa mu ga matakan da za a daukan ta yadda shi ba zai cutu ba jam'iyya kuma ba za ta cutu ba." In ji Yari.
Idan gwamna Muhammed Bello Matawalle ya koma APC gwamnonin PDP uku kenan suka koma cikin jam'iyyar cikin takaitaccen lokaci abin da ya sa manazarta al'amurran yau da kullum irinsu Kwamared Sagir Baba Nataionalist, ke ganin hakan ba zai taimaki siyasar kasar ba.
"Mene ne abin burgewa a ce gwamna ya canza jam'iyya a lokacin da jiharsa take fama da matsaloli daban-daban." A cewar Sagir Baba.
Karin bayani akan: APC, PDP, gwamnan, jihar Zamfara, Kotun Koli, Bello Matawalle, Abdullahi Umar Ganduje, Nigeria, da Najeriya.
Sai dai kuma duk da matsalar da tsohon gwamnan jihar Zamfara Alhaji Abdul'aziz Yari ya bayyana, ya ce shigar gwamna Muhammed Bello Matawalle APC alkhairi ne.
"Mu a jihar Zamfara, babu ko shakka za mu yi aiki da gwamna a jam'iyyance, muna ganin wannan in Allah ya yarda zai zama ci gaba da al'umar jihar Zamfara, kuma abu ne da muka yi marhaba da shi." Yari ya ce.
Daga kammala zaben shekarar 2019 zuwa yau gwamnoni hudu ne suka sauya Jam'iyya inda APC ta sami uku PDP kuma ta sami daya wanda wannan ya sa wasu ke ganin ya kamata a yi dokar haramta sauyin sheka a kundin tsarin mulkin Najeriyar.
Saurari rahoto cikin sauti daga Isah Lawal Ikara: