Tun bayan hallaka mutane goma sha tara da 'yan-bindiga su ka yi a garin Kadanya da ke Kutemeshi a Karamar hukumar Birnin Gwari, al'umar garuruwan da ke yankin sun dukufa wajen gudun hijira don tsira da rayukansu.
A karo na biyu an dakatar da taron manema labarai da gamayyar kungiyoyin Arewa (CNG) ta shirya a garin Kaduna, inda aka jibge jami’an tsaro tare da kame wasu shugabannin kungiyar.
Kungiyar Miyetti Allah ta gargadi ‘ya‘yanta da kar su dauki wani matakin ramuwa, game da harin da aka kai kan Fulani a garin Kurmin Bi na karamar hukumar Zangon Kataf.
Lamarin tsaro na ci gaba da tabarbarewa a daidai lokacin da hare-haren ‘yan ta’adda da masu satar mutane domin kudin fansa ke addabar wasu yankuna na jihar Kaduna.
'Yan Najeriya na ci gaba da kokawa game da matsalar tsaro a kasar musamman ma batun harin da 'yan bindiga suka kai kwanan nan a wata makantar kwana da ke garin Kankara a jihar Katsina.
Hadakar kungiyoyi matasa masu zaman kansu a Najeriya sun gudanar da wani taro, akan tabarbarewar tsaro a Arewacin kasar.
Ganin yadda ake alakanta matsalolin tsaro da sace mutane don neman kudin fansa ga Fulani a Najeriya, ya sa kungiyar ci gaban makiyaya da habaka al'adar su ta FUDECO shirya taron bayyana matsayin su game da irin wannan zarge-zarge.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci sabon sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya bada ta shi gudummawar wajen ganin an dawo da zaman lafiya da fahimtar juna.
A yayin da Amurkawa ke kakkabe shimfidar shiga fagen kada kuri'a zaben shugaban kasa, Wasu masu fashin baki kan harkokin yau da kullun a Najeriya na cigaba da yin tsokaci a kan zaben na Amurka.
Anyi bukin cika shekaru 50 na gidan tarihi na “Arewa House” dake Kaduna inda Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayana tarihi a matsayin sinadarin ci gaban al’umma.
Gwamnatin jihar Kaduna dake arewacin Najeriya ta kafa dokar hana zirga zirga ta sa’o’i 24 a cikin jihar, lamarin da yasa shugabannin addinai suka bayyana rashin amincewar su da wannan mataki da gwamnatin jihar ta dauka, suna cewa ba a kai ga wannan matsayi ba tukuna.