Litinin din nan ne ake cika kwanaki 80 da kai harin da 'yan-bindiga su ka yi a jirgin kasan Abuja-Kaduna, inda su ka sace mutane da dama kuma su ka kashe wasu.
Duk da bayanin gwamnatin jihar Kaduna game da taimakon da al'umamr garin Dogon noma su ka ce jirgin sama ya yiwa 'yan bindigar da su ka kai musu hari wanda gwamnatin ta musanta, shugaban kungiyar al'umamr Adara ya ce su ba su gamsu da bayanan gwamnatin ba.
Al'ummar yankin Birnin Gwari sun ce tun da hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna ta zama tarkon mutuwa to sun yanke shawarar kauracewa hanyar baki daya har sai mahukunta sun dauki mataki.
Kungiyoyi da al'umomi daban-daban na cigaba da Allah wadai da kisan da 'yan-bindiga su ka yiwa Harira mai dauke da juna biyu da 'ya'yan ta hudu a jahar Anambra.
A karshe dai 'yan-bindigan da su ka sace mutane a jirgin kasan Abuja-Kaduna sun bada wa'adin mako daya ga gwamnatin tarayya kan sako yaran wasu 'yan-bindigan da su ka ce idan ba haka ba, za su fara daukar mataki
Gwamnatin jahar Kaduna ta ce lamarin tsaro a fadin Jahar ya kara ta'azzara masamman ma ta adadin mutanen da 'yan-bindiga su ka kashe da kuma wadanda aka sace cikin watanni ukun farkon wannan shekarar
A yayin da zabukan shekarar 2023 ke kara karatowa, kungiyar 'yan jarida ta kasa reshen jihar Kaduna ta ce ba za ta lamunci sabawa aikin jarida don kambama 'yan siyasa ba.
A yayin da al'umar Musulmi ke bukukuwan sallar idi a fadin duniya, 'yan'uwan mutanen da 'yan-bindiga su ka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna sun ce su na cikin kunci da damuwa sannan kuma sun tabbatar da cewa labarin da ake yadawa na sako Sadiq Ango Abdullahi ba gaske ne ba.
Gwamnatin jahar Kaduna ta jawo hankalin al'umma game da rahoton dasa abubuwa masu fashewa a wasu sassan jahar Kaduna lokacin bukukuwan sallar dake tafe.
Ganin yadda ake yawan samun tashe-tashen hankula da rashin tsaro a wasu sassan jihar Kaduna da Najeriya baki daya ya sa kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN cewa lokaci ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi tsaye don magance matsalar tsaro a Najeriya.
Duk da gangarar karewar wa'adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta ce wajibi ne shugaban kasa ya ajiye mukamin shi saboda gazawar da ya yi na kare rayukan mutane da dukiyoyi.
Kwanaki sha biyar da kai harin jirgin kasan Abuja-Kaduna, 'yan uwan mutanen da aka sace sun ce lokaci ya yi da gwamnati ya kamata ta nemawa wadanda aka kama mafita tunda 'yan bindiga sun ce da gwamnati za su yi Magana.
Domin Kari