Sai dai sabuwar kungiyar mai suna Nomadic Rights Concern a turance ba za ta kare wadanda ke cikin harkar barna da fasadi ba.
Sabuwar kungiyar makiyayan da ta yi taron ta na farko a Kaduna, ta kaddamar da sabbin shugabannin ta kuma daya daga cikin iyayen kungiyar, Dr. Ahmed Mahmud Gumi, ya ce kungiyar adalchi za ta tabbatar domin samun zaman lafiya a Najeriya, ba nuna banbanchin kabila ba.
DR. Gumi ya ce an kirkiri sabuwar kungiyar makiyayan ne don banbance baragurbi da mutanen kwarai wanda hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a Najeriya.
Ya ce kungiyar za ta yi amfani da lauyoyi wajen ganin duk makiyayin da aka kama shi ba tare da hakki ba, ta karbo mai hakkin shi, wadanda kuma aka tabbatar sun yi laifi za ta taimaka wajen hukunta su.
Babban Sakataren kungiyar Fulanin Najeriya da ake kira Gan-Allah Fulani Development Association, Alh. Ibrahim Abdullahi na cikin iyayen wannan sabuwar kungiyar makiyaya, kuma ya ce idan ana son samun zaman lafiya sai an gane cewa matsalar tsaro ba daga kabila daya ta ke fitowa ba.
Alh. Abdullahi ya ce cikin harkar 'yan-bindigan da ke sace mutane akwai Hausawa da Yarabawa da Inyamurai da Fulani da ma sauran kabilu saboda akwai masu kai musu makamai da kwayoyi da kuma daukan kayan da su ka sata.
Fulani mata da maza daga yankunan Najeriya daban-daban ne dai su ka hada wannan kungiya kuma sun ce za su bi dukkan dokokin kasa wajen gabatar da ayyukan su.
Saurari cikakken shirin cikin sauti: