A ranar Asabar din wannan mako ne dai mutanen da 'yan-bindigan su ka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna za su cika watanni biyu a daji duk da cewa sun dan saki wasu daidaiku, kuma duk da kwashe wannan tsawon lokachi, 'yan-bindigan sun ce gwamnati ba ta yi musu abun da su ke nema ba.
'Yan-bindigan da su ka ki amincewa da tattaunawa da daidaikun iyalan wadanda su ka sace, sun kira shugaban kamfanin jarida Dessert Herald da ke Kaduna Malam Tukur Mamu wanda dama ya saba bin tawagar Dr. Ahmad Gumi zuwa daji don neman sulhu da 'yan-bindigan, kuma ya yiwa Muryar Amurka karin bayani.
Malam Tukur Mamu ya tabbatarwa Muryar Amurka cewa, dage sufirin jirgin kasan da gwamnati ta a ranar litinin ta wannan mako na da nasaba da wannan batu.
Dama dai tun farkon faruwar harin jirgin kasan, gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasuru Ahmed El-Rufa'i ya ce akwai yuwuwar barayin mutanen ba za su kula daidaikun iyalan wadanda su ka sace ba.
Tun bayan zanga-zangar nuna damuwa game da yunkurin dawo da sufirin jirgin kasan Abuja-Kaduna da 'yan-uwan wadanda aka sace su ka yi dai ba a kara jin duriyar su ba.
Saurari cikakken rahoton Isa Lawal Ikara cikin sauti: