Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Addinai Sun Gudanar Da Taron Zaman Lafiya A Kaduna


Gwamna El Rufai (Facebook/El Rufai)
Gwamna El Rufai (Facebook/El Rufai)

Ganin yadda ake yawan samun tashe-tashen hankula da rashin tsaro a wasu sassan jihar Kaduna da Najeriya baki daya ya sa kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN cewa lokaci ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi tsaye don magance matsalar tsaro a Najeriya.

Mataimakin shugaban Kungiyar Kiristoci CAN, reshen jahar Kaduna, Rabaren Chris Ange wanda ke jawabi wurin wani taron zaman lafiya a jahar Kaduna, ya ce zaman lafiya kadai ne zai ceci wannan kasa.

Rev Chris ya ce “Muna so mu yi magana da gwamnati ta tashi ta yi yaki sosai. Muna so mu samu zaman lafiya a Najeriya, shine zai bamu daman da zamu yi aiki da muke so. In muna so mu yi tafiya daga nan zuwa Sokoto ba tare da zaman lafiya ba, ba zamu iya yi ba, in muna so mu je mu ga iyayen mu a Legas ba zaman lafiya ba zamu je ba.”

Rev. Chris ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tashi haikan ya dauki duk matakan da suka dace domin a samu zaman lafiya a Najeriya.

Rabaren Father Joshua Achi shine shugaban kungiyar da ta shirya wannan taron zaman lafiyan da ya hada har da daliban makarantu da kuma kungiyoyi daban-daban, kuma ya yi bayanin hikimar da ke ciki.

Ya Kamata Jami'ai Su Yi Amfani Da Layukan Sadarwa Wajen Gano 'Yan Ta'adda - Ndumi
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:22 0:00

Ya ce sun kira wannan taro ne domin samun zaman lafiya a jihar su ta Kaduna da ma kasar Najeriya baki daya saboda in babu salama akwai damuwa. Ya ce sun gayyaci dalibai ne domin ilmantar dasu a kan wannan Magana ta salama tun suna cikin kurucciya.

Daliban da suka halarci taron da galibin su mata ne sun ce an kara musu ilimi a kan yadda zasu bada gudunmuwarsu ga samun zaman lafiya a Najeriya, haka zalika taron ya nuna musu yanda za su yi zumunci ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila ba.

Taron zaman lafiyan da ya hada mabiya addinai daban-daban da al'umar bangarorin jihar Kaduna ya tashi akan cewa dole ne kowa ya bada gudummawa wajen samar da zaman lafiya don cigaban kasa.

Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

XS
SM
MD
LG