Kasa da sa’o’i 48 da sanar da bai wa bankunan kasuwanci damar kayyade farashin kudadden waje musamman na dala da babban bankin Najeriya na CBN ya yi, masana a fannin tattalin arziki, 'yan kasuwar canjin bayan fage da sauransu, na ci gaba da bayyana mabambantan ra’ayoyi a game da matakin.
A wani zama da ta yi a karon farko bayan da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ayyana cire tallafin man fetur, hukumar NMDPRA ta bayyana wa dillalan man fetur cewa kofarta a bude take ga duk wanda ke bukatar samun lasisin shigowa da man fetur cikin kasar muddin zai bi ka’idodin da doka ta tanadar.
A jawabinsa na farko, shugaba Tinubu, ya yi murnar cika shekaru talatin da ‘yan kasar suka fita rumfunan zabe domin gudanar da zaben shugaban kasa da suke so a wancan lokaci, wanda zai jagoranci komawa tsarin mulkin farar hula na wakilcin jama’a sabanin mulkin soji da ake ganin na kama karya ne.
Injiniya Faruk Ahmed ya bayyana hakan ne a Wata Hira ta musamman da Muryar Amurka, inda ya yi kira ga 'yan Najeriya da su shiga farga tare da mika bukatar dilallan man fetur su buda gidajen mai, su rika sayar da man saboda kamfanin NNPCL ya tabbatar da cewa akwai wadataccen mai da zai ishi 'yan kasa
Kamfanin kasuwancin man fetur na Najeriya wato NNPCL ya tabbatar da cewa akwai wadataccen mai da zai ishi 'yan kasa na kimanin kwanaki 30 duk da cewa an fara ganin dogayen layukan mai tun da maraicen ranar Litinin,.
Sabon shugaban Najeriya da ya harbi rantsuwar kama aiki a ranar Litinin 29 ga watan Mayu, Bola Ahemd Tinubu, ya sha alwashin yin gagarumin garambawul da ta da komadar tattalin arzikin kasar ta hanyoyi daban-daban.
Kotun koli a Najeriya ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP ta shigar ta na kalubalantar tsayawar Sanata Kashim Shettima takara a mukaman siyasa biyu, wato amincewa da zama mataimakin shugaban kasa da kuma sayen tikitin neman kujerar Sanata a majalisar dattawan Najeriya.
Jim kadan bayan ci gaba da zaman sauraron kararrakin Zaben shugaban kasa na watan Fabrairu, a yau Litinin kotun ta yi watsi da bukatar da jam’iyyun Leba da PDP suka shigar ta neman a rika yada duk zaman kotun da za a yi kai tsaye a kafafen yada labarai.
A kwana ta hudu da fara zama, kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta dage zamanta na sharar fagge a karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar suka shigar gabanta zuwa ranar Alhamis, 18 ga watan Mayu, 2023.
A zaman da ta yi ranar Laraba 10 ga watan Mayu, kotun sauraron kararrakin kalubalantar nasarar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaben 2023 ta yi watsi da karar da jam’iyyar APP ta shigar bayan da lauyan da ke kareta ya ce sun janye karar.
Kasa da sa’o’i 48 da fara zaman share fagen sauraren shari’a a karar da jam’iyyun daban-daban suka shigar kan sakamakon zaben shekarar 2023, kotun ta dage zaman shari’ar da PDP ta shigar da hukumar INEC, APC, da Bola Tinubu zuwa ranar Alhamis 11 ga watan Mayu.
Kotun musamman ta sauraren kararrakin zaben shugaban kasar Najeriya da ke zama a Abuja ta fara shara Faggen zaman sauraren kararrakin zaben shugaban kasa da aka shigar a gabanta.
Kungiyoyin raya kasa sun yi taro domin tabbbatar da zaman lafiya a Najeriya, tabbatar da zaman lafiya da hadin kan 'yan Najeriya bisa la'akari da irin kalaman da wasu 'yan siyasa da basu ji dadin yadda sakamakon zabe ya kasance ba.
Babban bankin Najeriya ya ce yana ci gaba da buga sababbin takarkun kudi, sai dai har yanzu 'yan Najeriya na kokowa da cewa, suna cigaba da fuskantar matala wajen samun takadun kudin.
Karamin ministan albarkatun man fetur na Najeriya Timipre Sylva ya yi murabus daga mukaminsa a kasar domin neman sabon wa'adi a matsayin gwamnan jihar Bayelsa mai arzikin man fetur a yankin Neja Delta.
Domin Kari