Kungiyoyin fararen hula fiye da 30 ciki da cibiyar CISLAC dake fafutukar kare fararren hula da kuma sa ido a kan harkokin yaki da cin hanci da rashawa sun bayyana cewa kamata ya yi shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya fito kararra ya bayyana matsayinsa a game da mahimmancin aikin yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
Jagoran kungiyoyin fararren hulan wanda shi ne shugaban cibiyar CISLAC kuma wakilin kungiyar Transparency International a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani ne ya bayyana matsayin da suka dauka na yin kiran a kan bukatar shugaba Tinubu ya fito kai tsaye ya bayyana matsayinsa a game da batun yaki da almundahana a kasar.
Barrister Mainasara Kogo, fitaccen masanin kundin tsarin mulki a kasar, ya ce tsarin mulki ya wajabtawa duk wani jami’in gwamnati a kan ya yaki cin hanci da rashawa.
A cikin shawarwarin da suka bai wa gwamnatin shugaba Tinubu, kungiyoyin sun bukaci a kaddamar da dokar kariya ga jami’an EFCC da ICPC da saura cibiyoyin yaki da almundahana, sai kuma kare masu kwarmata bayanai a kasar, sai batun yadda za a aiwatar da dabarun yaki da cin hanci da rashawa na kasa da dokar 'yancin watsa labarai ta shekarar 2011 a duk jihohin tarayya ciki har da Abuja da dai sauransu.
Idan ana iya tunawa dai gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hau mulki ne da manyan alkawura 3 ciki har da batun yaki da cin hanci da rashawa, sai dai masu ruwa da tsaki na ganin ba a cimma nasara a kan wannan kuduri ba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: