Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Kori Karar Kalubalantar Tsayawar Kashim Shettima Takara A Mukamai Biyu


ABUJA: Kotun kolin Najeriya
ABUJA: Kotun kolin Najeriya

Kotun koli a Najeriya ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP ta shigar ta na kalubalantar tsayawar Sanata Kashim Shettima takara a mukaman siyasa biyu, wato amincewa da zama mataimakin shugaban kasa da kuma sayen tikitin neman kujerar Sanata a majalisar dattawan Najeriya.

A zaman da wasu alkalai biyar a karkashin jagorancin mai shari’a Adamu Jauro suka yi ranar Juma’a 26 ga watan Mayu ne kotun kolin ta zartar da wannan hukuncin, inda ta amince da matsayar kananan kotuna da suka bayyana cewa jam'iyyar PDP ba ta da hurumin shigar da irin wannan karar a gaban kotu, tana mai cewa PDP ta yi katsalanda ga ayyukan cikin gida na jam'iyyar APC tun da su ba mambobin jam'iyyar ba ne.

A yayin karanta hukuncin kotun, mai shari’a Adamu Jauro ya ba da umarnin jam’iyyar PDP ta biya tarar Naira miliyan biyu, duk da cewa kotu ta kori karar a bisa rashin cancanta, inda alkalan suka bayyana cewa karar da PDP ta shigar ta nemi ta sanya kotu cikin rudani ne kawai.

Lauyan masu kara Joe Agie mai mukamin SAN ya shaida wa Muryar Amurka cewa ba zasu dauki wani mataki na gaba ba saboda babu inda zasu iya zuwa bayan hukuncin kotun kolin.

Tuni dai kungiyoyin da ke mara wa jam’iyyar APC da ake kara a gaban kotu su ka yi ta nuna farin ciki a kan hukuncin kotun na ranar Juma’a.

Ambasada Ibrahim Abubakar da ke zama shugaban kungiyar magoya bayan jam’iyyar APC tare da hadin gwiwar sauran kungiyoyi magoya baya, ya ce godiya ta tabbata ga Ubangiji da ya basu nasara a kotu, saboda kotu ta fayyace abin da ake nufi da tsayawa neman takara a mukamai biyu kuma babu wanda aka yi wa rashin adalci a shari’ar, yana mai cewa kamata ya yi dukkan jam'iyyu su hada gwiwa da gwamnatin da za a kafa don ciyar da kasar gaba.

Shi ma jagora a wata kungiyar marawa jam'iyyar APC baya a matakin kasa, Ambassador Ibrahim Abubakar Batati, ya bayyana cewa abun farin ciki ne da bangaren shari’a ya fayyace abin da doka ta ce a game da karar da jam'iyyar PDP ta shigar tana kalubalantar dan takarar mataimakin shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar APC, Kashim Shettima.

Haka kuma, alkalan kotun kolin sun bayyana cewa ko da jam'iyyar PDP na da korafi kan yadda APC ta gudanar da zabukan fitar da gwaninta, dole ne PDP ta ci gaba da zama ‘yar kallo, inda suka kuma tunatar da jam'iyyar PDP irin wannan batu da ya taba faruwa a shekarar 1999, lokacin da Atiku Abubakar ya tsaya takarar gwamna amma daga baya ya koma ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ga Olusegun Obasanjo.

Idan ana iya tunawa dai jam'iyyar PDP ta shigar da kara a gaban kotun koli ne inda ta yi ikirarin cewa zaben Shettima a matsayin mataimakin dan takarar zababben shugaban kasa Bola Tinubu, ya saba wa tanadin sashe na 29 sakin sashe na 1, sashi na 33, 36 da 84 (1) (2) na dokar zabe ta shekarar 2022, amma hukuncin da kotun ta yanke ta jaddada cewa jam'iyyar adawa ba ta da wata hujja.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

XS
SM
MD
LG