Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubuwan Da Jawabin Tinubu Na Ranar Dimokuradiyyar Ya Kunsa


Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu

A jawabinsa na farko, shugaba Tinubu, ya yi murnar cika shekaru talatin da ‘yan kasar suka fita rumfunan zabe domin gudanar da zaben shugaban kasa da suke so a wancan lokaci, wanda zai jagoranci komawa tsarin mulkin farar hula na wakilcin jama’a sabanin mulkin soji da ake ganin na kama karya ne.

Jawabin dai ya kunshi, batun yin watsi da dokokin da ba su dace ba da ake amfani da su don rushe tsarin mulkin demokraɗiyya a kasar, inda shugaban ya ce mai dole ne a bi doka da oda waɗanda za a iya amincewa da su don tabbatar da adalci da ƙarfafa hukumomin gwamnati.

Haka kuma, shugaba Tinubu, ya ce an daidaita shekarun ritaya ga ma’aikatan bangaren shari’ar kasar na baya-bayan nan ne da nufin karfafa tsarin doka, wanda shi ne muhimmin ginshikin dimokuradiyya kuma yanzu aka fara gyara a kasar. Ya na mai cewa gwamnatinsa za ta habbaka tsarin mulkin dimokuradiyyar da zai samar da rabo mai kyau ga yan Najeriya wadanda su ne kashin bayan kasar.

Shubaga Bola Tinubu a tsaye yana magana (Hoto: Facebook/Tinubu)
Shubaga Bola Tinubu a tsaye yana magana (Hoto: Facebook/Tinubu)

Tinubu ya kara da cewa, za a yi adalci ga dukkan yan kasa ta bangaren zamantakewa da bunkasa tattalin arziki ga mutanen kasar, yaki da kawar da talauci da sauran matsalolin da suka addabi kasar.

Baya ga haka, Tinubu ya yi waiwaye a kan jawabinsa na ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata a yayin karbar mulki daga hannun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya karfafa tare da ba da muhimmanci ga shawarar gwamnatin da ta shude na cire tallafin man fetur tare da ba da himma ga yin amfani da kudaden da ake amfani da su wajen bada tallafin man fetur a wasu bangarorin da ake da bukata a kasar wanda wasu tsirarin mutane kawai ke cin moriyarsu a baya.

Jawabin Tinubu
Jawabin Tinubu

Shugaba Tinubu ya yarda cewa a wannan matakin da gwamnatinsa ta aiwatar za ta dora nauyi a kan dukkan yan Najeriya kuma ya san radadin da hakan zai janyo . Amma wannan mataki ne da ya zama dole ‘yan kasar su jure domin ceto kasarmu daga ci gaba da fadada cikin wani mumuman yanayi tare da kwace albarkatunmu daga hannun wasu tsiraru marasa kishin kasa.

Abun takaici shi ne zan roke ku ’yan kasa, ku kara sadaukarwa kadan domin cigaban kasarmu, kuma da amincewarku da imani da gwamnatinmu, ina tabbatar muku cewa sadaukarwarku ba za ta tafi a banza ba, in ji Tinubu.

A cewar Tinubu, gwamnatinmu za ta biya ku ta hanyar zuba jari mai yawa a bangaren sufuri, ilimi, samar da wutar lantarki na yau da kullun, kiwon lafiya da sauran ababen more rayuwa da za su inganta rayuwar jama’ar kasa baki daya kuma dimokuradiyyar da marigayi MKO Abiola ya mutu domin ita ce za ta inganta jin dadin jama’a fiye da bukatun kashin kai na masu mulki kuma wanda ake jagoranta za su samu Romon dimokuradiyya din kamar fafutukar da MKO Abiola ya bijiro da ita a fadin kasarmu a shekarar 1993.

Wutar lantarki
Wutar lantarki

Tinubu, ya roki ‘yan Najeriya da su sake sadaukar da kansu wajen karfafa wannan tsarin mulkin dimokuradiyya na ‘yantattun mutane wanda ya kasance hasken kasar a cikin shekaru 24 da suka gabata, musamman wadanda aka zaba a mukaman gwamnati a matakai daban-daban a bangaren zartaswa da na majalisa dole ne a jajirce wajen sadaukar da kai ga al’umma, tare da samar da ribar dimokuradiyya ta zahiri kamar yadda gwamnatinsa ta alkawarta a yayin gangamin yakin neman zabe.

Jawabin Tinubu
Jawabin Tinubu

Daga karshe, shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta sake jadada alkawarinta da sabunta kudiri na cika dukkan wani bangare na alkawurran da ta dauka a lokacin gangamin yakin neman zabe ga jama’a, kuma za mu tabbatar da daidaito da yin mulki cikin adalci, mutunta doka, da jajircewa wajen kare martabar al’ummar Najeriya a kodayaushe.

A bangaren soke zaben Marigayi Moshood Abiola, Tinubu yace, soke gagarumin nasarar da cif Moshood Abiola ya yi a zaben shugaban kasa karskashin rusasshiyar jam’iyyar Social Democratic Party wato SDP na ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993 da sojoji suka yi, zaben da ake gani shi ne mafi inganci da walwala a siyasar kasar, ya haifar da gwagwarmaya mai tsawo wadda ta kai ga komawa tsarin mulkin dimokuradiyyar da muke ciki a yanzu tun shekarar 1999.

Abiola
Abiola

Shugaba Tinubu ya kwatanta gwagwarmayar da marigayi Moshood Abiola da wasu jajirtattun yan kasa a waccan lokaci suka yi da tsoffin shuwagabannin da suka yi na adawa da mulkin mallaka.

Tinubu ya kuma nuna murna ga ranar ta yau da ta ci gaba da zama muhimmiya a tarihin al’ummar Najeriya, yana mai cewa ba wai yau kadai ba, a kowace ranar 12 ga watan Yuni, ta zama wata makoma mara iyaka da kasar za ta ci gaba da yin karfi kuma duk yan Najeriya za su rika tunawa da kansu cewa dimokuradiyyar da ke ci gaba da bunkasa ta zama ma’anar siyasar kasar wanda ba a cikin sauki aka same ta ba.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yana duba jami'an tsaro a bikin ranar dimokuradiyya a fadarsa
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yana duba jami'an tsaro a bikin ranar dimokuradiyya a fadarsa

A saukake za mu iya tunawa da sadaukarwa da Cif MKO Abiola, wanda ya sami nasara aka soke da zalunci kuma ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare muradun dimokuradiyya da kishin kasa ba tare da kakkautawa ba, kamar yadda ya ke alamta a zabinsa, ta 'yan kasarsa, a matsayin zababben shugabansu, in ji Tinubu.

Kazalika, Tinubu yace a kullum, a irin wannan rana, kasar zata rika tunawa da wasu jaruman neman tsarin mulkin dimokuradiyya da dama irin su marigayiya Kudirat Abiola, matar marigayi Cif Abiola, wadda aka yi wa kisan gilla a lokacin da ta ke fafutuka don nema wa al’umma mafita, sai Pa Alfred Rewane, daya daga cikin jaruman fafutukar neman yancin kai, sai kuma marigayi Manjo Janar Shehu Musa Yar'Adua (rtd) wanda gwamnatin mulkin soja ta yi ta taka shi a lokacin da yake fafutukar neman a koma tsarin dimokradiyya.

A wannan shekarar, Najeriya ta gudanar da zabe karkashin tsarin mulkin dimokuradiyya na bakwai a zagayowar zabukan da suka zama masu cike da tarihi tun shekarar 1999.

Tinubu ya ce an fafata da juna sosai a zaben waran Febrairu, zaben da shi kansa shaida ce mai kyau da ke nuna cewa dimokuradiyya tana nan a cikin Najeriya, inda yace duk da cewa wadanda suka samu nasara a zabuka daban-daban suna murna, wadanda suka fadi sun ji takaici, amma kyawun tsarin mulkin dimokuradiyya shi ne wanda ya yi nasara a yau zai iya yin rashin nasara a gobe kuma wanda ya fadi yau zai samu damar fafatawa da yin nasara a zagayen zabe na gaba.

Ga marigayi Cif MKO Abiola, wannan rana ta 12 ga watan Yuni ta zama ranar hutu ta kasa, kuma dimokuradiyya zata dawwama.

XS
SM
MD
LG