Fitaccen malamin addinin Musulunci a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi gargadin cewa ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda ba zai haifar da da mai ido ba.
Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya ta fara yiwa tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim tambayoyi a kan zargin almundahana da karkatar da dukiyar jama’a.
Kungiyar BudgIT ta bayyana cewa jihohin Najeriya 3 ne kadai daga cikin 36, za su iya biyan albashi bayan da gwamnatin tarayya ta cire Naira biliyan 172 daga asusun kananan hukumominsu.
Ministan Shari’a kuma antoni janar na tarayyar Najeriya, Abubakar Malami, ya bayyana cewa rahoton kwamitin da ofishinsa ya kafa ya yi nuni da cewa shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya yi ta harzuka magoya bayansa ta kafar rediyo Biafra.
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da cibiyar Amana Sanatorium mai kula da mutanen da suka yi tu’amali da miyagun kwayoyi a baya a jihar Kano.
Wasu gungun mutane dauke da makamai sun kai hari kan ofishin yan sanda da bama-baman man fetur a karamar hukumar Isiala Mbano ta jihar Imo da yammacin ranar Alhamis.
Rahotanni daga najeriya na nuni da cewa wasu mayaka da ake zargin masu mubaya’a ga tsagin kungiyar ISWAP da Ansaru ne ke da alhakin tarwatsa hanyar jirgin kasa data ratsa daga Abuja zuwa Kaduna.
Babbar kotun tarayya a birnin Abuja ta ki amincewa da bukatar da lauyoyin Nnamdi Kanu suka gabatar na maida shi gidan gyara hali dake yankin Kuje a Abuja.
A yayin da ake ci gaba da kiki-kaka kan badakalar takardun Pandora da suka fito da bayanan wasu jiga-jigai a duniya, hade da wasu 'yan Najeriya a ciki da ake zargi da boye bayanan kadarori da suka mallaka ta kasuwanci a gabar teku.
Rahotanni daga jihar Nasarawa sun yi nuni da cewa maharan da ake zargin 'yan bindiga ne da suka sace mutane 4 a jami’ar gwamnatin tarayya da ke Mararrabar Akunza sun tuntubi iyalansu tare da neman naira miliyan 25 a matsayin kudin fansa.
Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya wato CBN kuma dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019, Kingsley Moghalu, ya alakanta yawan barin kasar da matasa ke yi a halin yanzu ga matsin tattalin arziki da rashin kyawun yanayin rayuwa.
Wasu mahara da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari kan kasuwar kauye a Goronyo da ke karamar hukumar Goronyo a gundumar mazabar gabashin jihar Sakkwato.
Mai taimakwa shugaban Najeriya Muhamaddu Buhari kan sha’anin yadda Labarai, Femi Adeshina, ya bayyana cewa a tarihin kasar bai ga wani dan siyasa da ya kai mai gidansa shugaba Buhari farin jini a wurin jama’ar kasa daga yankuna daban-daban ba.
Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi kira ga jihohi da su sake nazari mai zurfi, su kuma yi Tunani kamar kasashe masu 'yancin cin gashin kai, ta yadda za su bunkasa samun kudaden shiga na cikin gida domin tafiyar da lamurransu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta 'yan yankin Naija-Delta, ta yi barazanar cewa dole ne yankin Arewa da yanzu haka ke mulkin kasar, ya jira har zuwa shekarar 2031, wato bayan shekaru 10 kenan, kafin ya sake samar da wani shugaban kasa.
Gwamnatin tarayyar Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta ta soma gudanar da taron bitar ayyukan ministocinta na tsakiyar wa’adin mulki na biyu a birnin taraya Abuja.
Babban lauya a Najeriya kuma mai mukamin SAN, Femi Falana, ya nemi ministan shari’a kuma antoni janar na tarayyar kasar, Abubakar Malami, da ya karbo bashin dala biliyan 62 da kamfanonin man fetur na duniya 6 ke bin kasar a cikin wata wasika.
Wasu mazauna jihar Zamfara da suka kunshi kabilu daban-daban sun hada kai guri daya suka gudanar da addu’ar neman dauki kan matsalar tsaro da ke kara kamari a jihar.
Rundunar hadin gwiwar ‘yan sanda da 'yan sa kai a dajin Tsibiri da ke jihar Zamfara sun mika mutanen da suka ceto daga hannun 'yan bindiga ga gwamnatin jihar a aikin ci gaba da aiwatar da sabbin matakan yaki da batagari a jihar.
Sanata Adamu Bulkachuwa mai wakiltar mazabar jihar Bauchi ta Arewa ya bayyana cewa ba bu wani banbanci tsakanin 'yan fashin daji da' yan ta’adda domin duk suna aiki ne iri daya.
Domin Kari