Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata Malami Ya Aiwatar Da Umarnin Karbo Bashin Dala Biliyan 62 Da Najeriya Ke Bin Wasu Kamfanonin Mai 6 -Falana


Malami, hagu da Falana, dama
Malami, hagu da Falana, dama

Babban lauya a Najeriya kuma mai mukamin SAN, Femi Falana, ya nemi ministan shari’a kuma antoni janar na tarayyar kasar, Abubakar Malami, da ya karbo bashin dala biliyan 62 da kamfanonin man fetur na duniya 6 ke bin kasar a cikin wata wasika.

A cikin wasikar mai dauke da ranar 8 ga watan Oktoba da muke ciki, Falana ya ce kotun koli a shekarar 2018 ta umarci gwamnatin tarayya da ta gaggauta karbo bashin na dala biliyan 62 kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Sai dai, a bisa yadda karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, ya bayyana da alama gwamnatin tarayya ba ta ba da himma ga aikin dawo da kudadden ba, in ji Falana.

Falana dake jagorantar tawagar lauyoyi ne ga farfesa Omotoye Olorode da Jaye Gaskia na Jam'iyyar Alternative Political Movement wato PAPM wanda suka rubuta wasikar ga ministan shari’a a madadin su.

A cewar Falana, wadanda ya ke wakilta sun umarce shi da sauran lauyoyin da su ke aiki tare da su tunawa gwamnati cewa ba ta aiwatar da hukuncin kotun koli wanda ta yanke a ranar 20 ga watan Oktobar shekarar 2018 ba.

A cikin hukuncin na kotun kolin na umarci gwamnatin tarayya da ta hanzarta daukar matakan dawo da duk kudaden da aka rasa ga kamfanonin hakar mai da amfani da su saboda kuskuren tsarin raba riba tun daga watan Agustar shekarar 2003.

Kazalika, hukuncin kotun kolin ya nemi a gaggauta biyan tsabar kudi na dala biliyan 62 da kamfanonin mai na kasashen duniya shida ke bin gwamnati tare da hadin gwiwar kamfanin NNPC.

Kamfanonin man kasashen duniya da Najeriya ke bin kudadden sun hada da kamfanin Shell, Mobil, Chevron, Agip Najeriya, TotalElf Najeriya da kuma kamfanin Man Fetur na pan Ocean.

Falana ya ce abin takaici ga wanda ya ke wakilta shi ne yadda karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Silva, ya bayyana a fili cewa ai sun dai fara tattaunawa kan dawo da kudin amma sai an yi la'akari da cewa an rasa damar dawo da kudin da aka samu a lokacin baya.

Falana ya ruwaito Timipre Sylva na cewa babu wanda zai iya fitar da irin wannan tsabar kudin da ya kai dala biliyan 62 ba a yanzu inda ya ce ana iya samun wani abu daga ciki amma ba dala biliyan 62 ba don an riga an rasa damar yin hakan.

Don haka ne Falana ya rubutawa Malami wasika a madadin wadanda ya ke wakilta saboda ministan shari’a ya yi amfani da ofishin sa don tabbatar da cewa an dawo da adadin dala biliyan 62 daga kamfanonin man fetur na duniya 6 tare da saka su cikin asusun gwamnatin tarayya ba tare da wani jinkiri ba, in ji shi.

Haka kuma, Falana ya ce muddin antoni janar na tarayyar Najeriya ya gaza aiwatar da umarnin kotun koli za’a tilasta wa wadanda suke karewa su tunkari babbar kotun tarayya kasar don neman umurni mai karfi kan sa ya aiwatar da hakan.

XS
SM
MD
LG