Hukumar NRC mai kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya dai ta dakatar da ayyukan zirga-zirgar jirgin kasa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna bayan da rahotanni su ka yi nuni da cewa wasu 'yan ta'adda sun dasa bam a wani sashen layin jirgin, lamarin da ya kusa haddasa mumuna hatsari.
Haka kuma maharan sun kara tarwatsa wani sashen layin dogon da washe garin ranar Alhamis inda suka sake yin mummunar barna a kan layin, abin da ya tilastawa hukumar NRC dakatar da ayyukan jigilan fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna.
A yayin fitar da sanarwa a game da lamarin, hukumar NRC ta bayyana harin a matsayin babbar barna, lamarin da masana tsaro ke zargin yan ta’adda da aikatawa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wasu majiyoyin tsaro na cewa wasu mayaka da ake zargin masu mubaya’a ga tsagin kungiyar ISWAP da Ansaru ne ke da alhakin tarwatsa hanyar ta jirgin kasa.
Tuni dai yan Najeriya da dama suka fara tofa albarkacin bakinsu a game da barnar da wadanda ake zargin mayakan da ke mubaya’a da ISWAP da Ansaru suka kai.
A shafinsa na Tuwita, Sanata Shehu Sani wanda ya wakilci jihar Kaduna ta tsakiya a majalisa ta 8 ya bayyana cewa dakatar da ayyukan layin dogo da hukumar NRC ta yi shine mafi a’ala a yanzu, kuma ya kamata a dauki matakin gaba na sanya na'urori masu gano duk wani abu mai fashewa da aka dasa a kan layin dogon.
Shehu Sani ya kara da cewa wani matakin kuma shi ne tafiya Kaduna da jirgin sama zuwa birnin na Kaduna muddin gwamnati zata tabbatar da tsaro kan hanyar zuwa filin tashi da saukar jiragen saman na Kaduna.
Saidai sakon da sanata Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na Tuwita bai ma wasu yan kasar dadi ba inda wasu ke ganin cewa talakawa ba za su iya bin hanyar sufurin jirgin sama ba domin yana da tsadar gaske a wajensu.
Mal. Suleiman Ahmad, mai taimakawa sanata Shehu Sani na a bangaren lamurran siyasa da harkokin jama'a, yayi bayani kan yanayin da suka tsinci kan su a yayin tafiya a jirgin safe daga Kaduna zuwa Abuja.