Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Da 'Yan Banga Sun Ceto Mutane 187 Daga Hannun ’Yan Bindigar Zamfara


'Yan Sanda A Jihar Zamfara
'Yan Sanda A Jihar Zamfara

Rundunar hadin gwiwar ‘yan sanda da 'yan sa kai a dajin Tsibiri da ke jihar Zamfara sun mika mutanen da suka ceto daga hannun 'yan bindiga ga gwamnatin jihar a aikin ci gaba da aiwatar da sabbin matakan yaki da batagari a jihar.

Mutanen da aka ceto da suka hada da maza, mata da kananan yara da adadinsu ya kai 187, sun fito ne daga kananan hukumomin jihar uku kamar yadda SP Muhammad Shehu, jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar ya bayana a cikin wata sanarwar da ya fitar.

Mutanen da aka kubutar sun shafe makwanni da dama a hannun batagarin kuma sun fito ne daga garuruwan Rini, Gora, Sabon Birni da Shinkafi da ke kananan hukumomin Bakura, Maradun da kuma Shinkafi.

Sanarwar rundunar yan sandan jihar ta kara da cewa bayan gudanar da bincike mai zurfi ne aka sami nasarar kubutar da mutanen 187 ne ba tare da wasu sharudda ba.

Mutanen da yan sandan jihar Zamfara ta kubutar daga hannun yan bindiga.
Mutanen da yan sandan jihar Zamfara ta kubutar daga hannun yan bindiga.

Wannan nasarar da yan sanda suka samu a jihar Zamfara na da nasaba da aikin aiwatar da sabbin matakan tsaro da gwamnatin jihar Zamfara ta ke dauka wanda masana ke ganin matakin na haifar da da mai ido.

Baya ga dawo da layukan sadarwa a jihar, ’yan sanda da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro na ci gaba da kai farmaki kan maboyan ’yan bindiga a sassan jihar daban-daban, don kawar ayyukan ta’addanci da sauran muggan laifuffuka daga jihar.

Mutanen da yan sandan jihar Zamfara ta kubutar daga hannun yan bindiga.
Mutanen da yan sandan jihar Zamfara ta kubutar daga hannun yan bindiga.

Da maraicen ranar Alhamis ne rundunar ’yan sandan Jihar ta Zamfara ta mika mutanen da aka ceto ga gwamnatin jihar.

Da yake karbar mutanen da aka ceto, gwamnan jihar Bello Matawalle, wanda ya sami wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe, ya yi godiya ga dukannin hukumomin tsaro da suka hada da ’yan sanda a jihar a bisa namijin kokari da sadaukarwa wajen aikinsu domin tabbatar da samar da tsaro da zama lafiya a jihar.

Idan ana iya tunawa, tun bayan kaddamar da sabbin matakan tsaro a jihar ta Zamfara ne ’yan bindiga da dama da da yan gari masu hada baki da su ke ta shigan hannu, kuma tuni aka soma gurfanar da wasunsu a gaban kuliya tare da ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi.

Masanin tsaro da sha’anin diflomassiyar kasa-da-kasa, Kabiru Adamu, ya yi kira da gwamnatoci a dukkan matakai su dauki matakan tabbatar da hukunta masu laifi kamar yadda doka ta tanadar.

XS
SM
MD
LG