Shugaban kamfanin kasuwancin man fetur na Najeriya wato NNPC, Mal. Mele Kyari, ya yi karin bayani a game da yadda aka shigo da gurbataccen man fetur mai sinadarin Methanol da ya wuce kima daga kasar Belgium ba tare da an gano shi ba da kuma kamfanonin da suka shigo da shi.
Shugaban kula da dokokin ma'aikatar man fetur ta Najeriya, Malam Faruk Ahmed, ya yi cikakken bayani a game da akasi da aka samu a game da gurbataccen man fetur a wasu sassan kasar.
Majalisar zartaswar tarayyar Najeriya ta amince da shirin gyara kasafin kudin shekarar 2022 biyo bayan gyare-gyaren farko da majalisar dokokin kasar ta yi kan kudirin kasafin kudin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a shekarar 2021.
Wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun yi awon gaba da wani dan' uwan tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan a cikin gidansa dake birnin Yenagoa na jihar Bayelsa.
A kwanan nan gwamna Matawalle ya kai wa shugaba Buhari ziyara a fadarsa inda suka gana kan batun tsaro.
Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a birnin tarayya Abuja a yau Litinin inda ta ce gwamnatin kasar ta dage shirin cire tallafin man fetur har sai an bada sanarwa.
Jiga-jigan mata mambobin jam’iyyar APC mai multi ciki har da uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, sun ce suna shirye tsaf don jan ragamar mulki a kasar.
Tun bayan kashe wasu ma’aikata hudu a wajen hakar ma’adinai da wasu ‘yan bindiga suka yi a kauyen Dong dake karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato, al’umman garin suka fara zaman dar-dar sakamakon abun da ka je ya dawo.
Kasa da mako biyu bayan janye yajin aiki da yan adaidaita sahu suka shiga sakamakon kari a farashin da su ke biya na rijista, gwamnatin jihar kano ta rage kudin rijista a wata matsaya da ta cimma da kungiyar matukan.
Gabanin babban taron jam’iyyar APC mai mulki da aka tsaida gudanarwa ranar 26 ga watan Fabrairui, an rage adadin manyan jiga-jigan jam’iyyar dake neman shugabancin jam'iyar ciki har da gwamnoni da kuma wadanda ke fadar shugaban kasa.
Babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja a Najeriya ta dage zaman shari'ar Nnamdi Kanu shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu.
Daya daga cikin tawagar lauyoyin Nnamdi Kanu ya ce karin tuhume-tuhume da gwamnatin Najeriya ta yi cikin kasa da sa’o’i 24 kafin zaman bai dace ba.
Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa-NEC, Farfesa Attahiru Jega, ya bukaci majalisar dokokin Najeriya da Shugaba Muhammadu Buhari du gaggauta zartar da kudirin gyara dokar zaben ta shekarar 2021 zuwa doka.
Gwamnatin Najeriya ta bukaci kasar Saudiyya ta dage takunkumin hana zirga-zirgar da ta sanya wa matafiya ‘yan Najeriya biyo bayan bullar nau’in Omicron na cutar korona birus a kasar Afrika ta Kudu da aka gano a tsakanin wasu matafiya da aka ce sun ziyarci Najeriya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba rundunar sojin kasar umarni su yi amfani da karfi wajen kawo karshen ‘yan bindigar da ke kashe-kashen al’ummar da basu ji ba basu gani ba, da kuma masu garkuwa da mutane a Jihar Neja.
Wasu yan arewacin Najeriya ciki har da matasa da ke zaune a cikin kasar da ma mazauna kasashen wajen sun fara amfani da kafafen intanet wajen neman taimakon kudi, kayan abinci da sutura ga ‘yan gudun hijirar jihar Zamfara da suka rasa muhallansu sakamakon ayyukan 'yan bindiga.
A yayin da direbobin babura masu kafa uku da aka fi sani da a daidaita sahu suka shiga yajin aikin gamagari a yau Litinin a jihar Kano, dubban fasinjoji sun shiga tsaka mai wuya a kan tituna inda su ke takawa zuwa wuraren aiki da sauran hidimominsu.
Duk da cewa an kubutar da wasu dalibai 30 da malami guda da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a kwalejin Birnin Yauri na jihar Kebbi watanni shida da suka gabata, ba’a iya tantance adadin daliban da suka rage a hannun 'yan bindigar ba.
Gwamnan Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana neman wasu mutane 19 dake gudanar da ayyukan tace danyen mai ba bisa ka'ida ba ruwa a jallo.
Domin Kari