Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar Da Batun Cire Tallafin Man Fetur Zuwa Wani Lokaci


Ministar Kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed (Instagram/ Zainab Shamsuna
Ministar Kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed (Instagram/ Zainab Shamsuna

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a birnin tarayya Abuja a yau Litinin inda ta ce gwamnatin kasar ta dage shirin cire tallafin man fetur har sai an bada sanarwa.

Ministar kudin Zainab Ahmed ta bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a majalisar dokokin kasar wanda aka kamalla da yamman nan.

An dai kira wannan taron ne a gaban shugaban majalisar dattawa, sanata Ahmad Lawan.

Taron dai ya sami halartar karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, da kuma shugaban kamfanin man fetur na Najeriya mai zaman kan sa wato NNPC, Mele Kyari, da dai sauransu kamar yadda mai magana da yawun shugaban kamfanin NNPC, Mal. Garbadeen Abdul-aziz ya shaida mana.

Ministar Kudi dai ta kara da cewa tun farko, gwamnatin tarayya ta na da shirin cire tallafin man fetur daga watan Yulin wannan shekara ta 2022.

A cewar Zainab Ahmed, hakan ne ya sa aka samar da isasshen tanadi a cikin kasafin kudin kasar na shekarar 2022 domin biyan tallafin har zuwa watan Yuni wanda hakan ya nuna cewa daga watan Yuli, ba za’a cire tallafin.

Gwamnati dai ta yi wannan tanadin ne kafin zartar da dokar masana’antar man fetur wato PIA wadda ta nuna cewa gwamnati zata cire hannunta daga ayyukan kayyade farashin man fetur da ba wa kamfanin NNPC ikon jagorancin kamfanin ba tare da katsalanda ba.

Haka kuma, kafin zartar da kudirin masana’antar man fetur zuwa doka, gwamnati ta koma ta yi gyara a tsarin kasafin kudi don dakatar da cire tallafin na man fetur.

Sai dai bayan an zartar da kasafin, gwamnati ta yi shawarwari da masu ruwa da tsaki da dama, inda aka bayyana cewa lokacin da aka sanya na yiyuwan cire tallafin man fetur din zai iya kawo matsala.

Zainab ta ce gwamnati ta gano cewa a zahiri, har yanzu ana samun hauhawar farashin kayayyakin masarufi kuma cire tallafin zai kara dagula lamarin da kuma kara sanya wa ‘yan kasa cikin matsi.

Lamarin da gwamnati ke ci gaba da tattaunawa a halin yanzu da kuma tuntubar juna ta fuskar samar da matakai da dama da zasu taimaka wajen rage radadin da yan kasa ka iya ji sakamakon cire tallafin.

Daya daga cikin wadannan matakan da gwamnati zata dauka sun hada da fitar da aikin tace man fetur a matatun da ake da su cikin gida da kuma gina sabbi wanda zai rage yawan tattacen mai da za’a rika shigowa da su cikin kasar.

Lamarin da ya kai ga gwamnati ta ga bukatar komawa majalisar dokokin kasar domin a gyara kasafin kudin da kuma samar da karin tanadin tallafi daga ranar 22 ga watan Yuli zuwa duk lokacin da gwamnati ta amince ya dace da fara cire tallafin baki daya.

Don haka shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan ya bukaci kungiyoyin kwadago da suka shirya yin zanga-zangar lumana a kasar don nuna rashin amincewar su da yiyuwar cire tallafin a watan Febrairu mai zuwa da su yi watsi da shirin na su a fadin kasar saboda ba bukatar hakan.

An dade ana kai ruwa rana kan batun cire tallafin na man fetur a Najeriya inda a shekarar 2021 gwamnati ta yi ta shelar zata cire tallafin don yadda tsiraru munane ne kawai ke cin moriyan hakan ba ba talakawa ba.

XS
SM
MD
LG