Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata Shugaba Buhari Da Majalisun Kasar Su Gaggauta Zartar Da Kudirin Gyara Dokar Zabe Zuwa Doka - Jega


Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, Farfesa Attahiru Jega.
Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, Farfesa Attahiru Jega.

Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa-NEC, Farfesa Attahiru Jega, ya bukaci majalisar dokokin Najeriya da Shugaba Muhammadu Buhari du gaggauta zartar da kudirin gyara dokar zaben ta shekarar 2021 zuwa doka.

Jega ya ce amincewa da zartar da kudirin zuwa doka zai taimaka matuka wajen gyara ingancin zabe a Najeriya.

Don haka ne tsohon shugaban hukumar ta INEC, ya bukaci gwamnati da ta yi duk mai yiwuwa don ganin kasar nan ta shiga zabe mai zuwa da wani sabon kudiri.

A cewar Jega, Najeriya za ta shiga kyawun yanayi idan har ta shiga sha’anin zabe mai zuwa da sabuwar dokar zabe wadda za ta kara inganta shirye-shirye da gudanar da zabuka masu sahihanci.

Jega ya bayyana hakan ne a yayin wani zauren tattaunawa kan kudirin gyara dokar zabe ta shekarar 2021 da aka gudanar a babban birnin tarayyar kasar Abuja a ranar Lahadi.

A yayin da ake ci gaba da tafka muhawara kan zaben fidda gwani na kai tsaye wanda aka fi sani da direct primaries a turance. Farfesa Jega ya bayyana cewa, kudurin gyara dokar zaben ya kunshi sabbin gyare-gyare da dama da ke da matukar muhimmanci ga ingancin tsarin zabe kuma yana ganin ya kamata a mayar da hankali a kan hakan.

A halin da ake ciki dai an gabatar da shawarwari 36 game da kudirin da hukumar INEC ta gabatar ga majalisar dokokin kasar inda 31 daga cikinsu an amince da su ba tare da gyare-gyare ba.

A cewar farfesa Jega, gyare-gyaren su ne na farko a cikin shekaru 12 da suka gabata, kuma hana amincewa da kudirin bisa ga wani sashi da ba’a amince da su ba zai kawo cikas ga aikin hukumar INEC ta yadda zata shirya zabe yadda ya kamata la’akari da zabe mai zuwa.

Tsarin doka mai kyau yana taimakawa wajen samar da zabuka cikin gaskiya kuma ingancin zabe na taimakawa wajen inganta tsarin mulkin dimokuradiyya da shirye-shirye da gudanar da zabe a dimokuradiyyance, in ji Jega.

Haka kuma, Jega ya ce akwai wasu abubuwa na asali wadanda za su taimaka wajen samun ingancin zabe, kuma kamata ya yi a zartar da kudirin da ya kunshi dimbin gyare-gyare, kuma a watsar da batun zaben fidda gwani na kai tsaye, a yi tunani sosai a kai.

Tun daga shekarar 2010, Najeriya ba ta sami wasu gyare-gyare a cikin tsarin dokokin zabe ba har zuwa yanzu.

Idan ana iya tunawa dai, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ki amincewa da kudirin dokar ne a watan Disambar shekarar 2021 a bisa dalilin tsadar gudanar da zabukan fidda gwanin kai tsaye, kalubalen tsaro, da yiwuwar dakile magudin zabe da ‘yan siyasa ke yi a kasar.

Kazalika, a wata hira ta musamman da ya yi da gidan talabijin na Channels a baya-bayan nan, shugaba Buhari ya lura cewa idan har ya amince da kudirin, dole ne a yi sauye-sauye da za su hada da karin ‘yan takarar da za su rika shiga zaben fidda gwani da ba na kai tsaye ba, zaben fidda gwani a kaikaice ga tsarin zaben wanda zai yi zabe, sabanin na kai tsaye. yanayin kai tsaye a matsayin zabi ɗaya tilo don gudanar da zabe na jam'iyyun siyasa.

Kamata ya yi a ba wa yan kasa zabi ta hanyoyi daban-daban don bai dace ba a cusawa yan kasa ra’ayi ba a dimokuradiyyance, in ji Buhari.

XS
SM
MD
LG