Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa an ceto akalla mutane dubu 2,155 daga hannun ’yan bindiga da su ka yi awon gaba da su a jihar a cikin wata hudu da suka wuce.
Gwamnatin ta ce cikin mutanen da aka ceto akwai daliban makarantun firamare, sakandare da kuma matan aure da kananan yara da dama.
Gwamnatin dai ta jinjinawa sojoji a game da yadda suka kara kaimi a aikin tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma da suke yi.
Kwamishinan yada labaran jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, ya ce an kubutar da mutanen ne cikin watanni hudu daga watan Satumban shekarar 2021 zuwa watan Janairun shekarar 2022 da muke ciki kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Dosarar ya kara da cewa an sami nasarar ceto mutanen ne a bisa hadin gwiwar hukumomin tsaron kasar ciki har da sojojji inda suka yi ta fatattakar ayyukan ’yan bindiga da ya ki ci ya ki cinyewa a jihar.
Daya daga cikin ayyukan da hukumomin tsaron su ke yi a Dajin Gando ya sa ’yan bindiga ya rage karfin miyagun iri a jihar kamar yadda Dosara ya bayyana kuma gwamnati na da kwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba za a kawo karshen ayyukan ta’addanci a cihar baki daya.
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, dai na aiki wajen tabbatar da samuwar zaman lafiya da tsaro a fadin jihar, in ji Dosara.
A baya-bayan nan ma sai da gwamnan jihar Zamfara gwamna Matawalle ya kai ziyara ga shugaba Buhari a fadar Aso Rock inda ya yi masa bayanin yanayin tsaron jihar ke ciki da kuma matakan da gwamantin jihar take dauka domin magance su.
Matsalolin 'yan bindiga dake addabar al’umma yankin arewa maso yamma da tsakiya abu ne da ya ki ci ya ki cinyewa musamman a kwanakin baya-bayan nan inda miyagun ke far wa al’umma da basu ji ba su gani ba musamman a jihar Zamfara tamarin da gwamnati a matakan jiha da tarayya ke cewa su na iya bakin kokarin su don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.