Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KANO: An Kammala Taron Bada Horon Sanin Makamar Aiki Ga Sabbin ‘Yan Majalisar Dokoki


Taron Bada Horo Kan Sanin Makamar Aiki Ga Sabbin ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano
Taron Bada Horo Kan Sanin Makamar Aiki Ga Sabbin ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta shirya taron sanin makamar aiki a wani bangare na shirye-shiryen kaddamar da sabuwar Majalisar ta goma da za a gudanar ranar Talata makon gobe.

KANO, NIGERIA - An gudanar da taron ne karkashin jagorancin Alhaji Lawan Badamasi tsohon akawun Majalisar dokokin ta Kano wanda ya bayyana cewa, manufar taron ita ce ilimantar da sabbin wakilan game da sha’anin Majalisa da kuma zaben shugabanni.

A hirar shi da Muryar Amurka, tsohon akawun Majalisar ya kara da cewa, sun shirya taron ne "domin nusar da cewa, kafin a zo zaben shugabannin Majalisa, wato shugaba da mataimakin sa da sauran jagorori, su lakanci yadda ake zaman Majalisa da jefa kuri’a a yayin zabe bayan gabatar da kudiri. Kuma an nuna musu yadda ya kamata su rinka shiga ta mutunci dama yadda mutum zai yi magana a zauren Majalisa”

Taron Bada Horo Kan Sanin Makamar Aiki Ga Sabbin ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano
Taron Bada Horo Kan Sanin Makamar Aiki Ga Sabbin ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano

Yayin da wadansu daga cikin ‘yan Majalisar dokokin ta Kano suka sake somawa Majalisar, wadansu daga cikin wakilan kuwa sabbin zuwa ne.

Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara wanda ya ke sabon wakili ne daga mazabar Gezawa, ya ce “mun fahimta mun gamsu da abin da aka koya mana kuma zamu yi aiki da abin da muka koya. Mun zo Majalisa ne domin gabatar da bukatun al’ummar mu kuma zamu iya kokari domin ganin cewa, bukatun sun biya”

Shi kuwa, Hon. Lawan Hussaini na Jam’iyyar NNPP daga mazabar Dala cewa ya yi “yanzu dama ta fadada, domin ina cikin Jam’iyya da ta kafa gwamnati kuma take da rinjaye a zauren wannan Majalisa ta dokoki, sabanin a baya da nake bangaren marasa rinjaye”

Taron Bada Horo Kan Sanin Makamar Aiki Ga Sabbin ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano
Taron Bada Horo Kan Sanin Makamar Aiki Ga Sabbin ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano

Sai dai Hon. Musa Ali Kachako na Jam’iyyar APC wanda ya koma Majalisar karo na uku ya ce komawarsa bangaren hamayya bai karya langwan sa ba.

Ya ce “hakan ba zai karya lagon matsayi na a Majalisa ba, ba zai fitar da ni daga Majalisa ba, babu abin da zai karya min gaba. Duk abin da ya zo Majalisa muddin ba ya kan tsari da doka zamu kalubalance shi bisa hujjoji na doka da ka’ida kuma hakan baya nufin hamayya ko adawa”

Hakan dai na nuna alamun yuwuwar faruwar zazzafar mahawara a zauren Majalisar dokokin ta Kano bayan kaddamar da ita a makon gobe, duk da cewa, daga cikin mambobi 40 na Majalisar Jam’iyyar NNPP da ta kafa gwamnati na da wakilai 23 yayin da APC ke da wakilai 17.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari cikin sauti:

 An Kammala Taron Bada Horo Kan Sanin Makamar Aiki Ga Sabbin ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

XS
SM
MD
LG