A shirye-shirye ta na gudanar da aikin Hajjin shekarar 2024, hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON ta bukaci maniyyata da su ajiye Naira miliyan 4.5 a matsayin kudin ajiya mafi karaci a asusun su na tafiya domin su biya kudin kujera idan lokaci ya yi.
Hukumar ‘yan sandan birnin Yamai ta umurci jagarorin masu zanga-zangar adawa da zaman sojan Faransa a kasar su mutunta doka, bayan rahotanni sun ce wasu na fakewa da sunan zaman dirshan din don tafka ta’asa, ciki har da yi wa mata fyade.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya ya shaidawa shugaban sojojin Gabon cewa hukumomin Majalisar Dinkin Duniya a shirye suke su tallafawa kasar yayin da take kokarin komawa kan tsarin mulki bayan juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin iyalan Bongo na tsawon shekaru 56.
‘Yan takarar manyan jam‘iyyun adawa a Najeriya sun ce za su sake daukaka kara kan hukuncin wata kotu da ta tabbatar da nasarar Bola Tinubu a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Fabrairu, inda suka yi ikirarin cewa an tafka magudi akwai kuma kura-kurai, in ji lauyoyinsu.
Akalla mutum 16 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata a ranar Laraba, bayan da Rasha ta yi luguden wuta kan wata kasuwa a wani birni a gabashin Ukraine, in ji jami'ai.
Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun ba da sanarwar kama tufafin sojan Burkina Faso a cikin motar wani sojan Faransa lokacin da ya ke kokarin shiga ofishin jakadancin Faransar a birnin Yamai.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi a Najeriya ya ce gwamnati da kungiyar kwadago sun cimma matsaya cewa ba za a yi yajin aiki ba har nan da tsawon mako biyu yayin da gwamnati ke kokarin duba korafe-korafensu.
Majalisar dokokin jihar Legas ta kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike akan wani yaro dan shekaru 12 da ke kwance a asibitin koyarwa na jihar bayan da karamin da hanjinsa ya bace bayan wata tiyata da aka masa a asibitin.
Kasar Faransa ta fara tattaunawa da wasu jami’an sojin Nijar kan janye wasu sojojinta daga kasar da ke yammacin Afirka bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yuli, in ji jaridar Le Monde a ranar Talata.
‘Yan siyasa da jami’an fafutuka a Jamhuriyar Nijar sun fara maida martani bayan da Firai Ministan Gwamnatin rikon kwaryar kasar ya sanar cewa Gwamnatin da soja suka hambarar a watan Yulin da ya gabata ta ci dimbin bashi daga ciki da wajen kasar.
Uwargidan shugaban Amurka Jill Biden ta kamu da cutar COVID-19 kuma a halin yanzu tana fama da alamu masu sassauci, in ji Fadar White House a ranar Litinin.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin ta bukaci dala biliyan 1 don taimaka wa wadanda ke gudun hijira a Sudan, inda ta ce tana sa ran sama da miliyan 1.8 za su tsere zuwa kasashe makwabta biyar a karshen shekara.
Najeriya na tunanin neman zama mamba a kungiyar kasashe mafiya karfin tattalin arziki ta G20 bayan wani tuntuba da ya yi kan alfanun shiga kungiyar da akasin hakan a cewar kakakinsa.
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ba da sanarwar sake bude sararin samaniyar kasar ga wani rukunin jiragen sama da nufin bai wa matafiya damar zirga-zirga tsakanin kasar da sauran kasashen duniya.
A ranar 30 ga watan Agusta, mintuna kadan bayan sanarwar Bongo ya lashe zabe, sojoji karkashin jagorancin Janar Oligui Nguema ya karbe mulki.
Kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya RIFAN, ta ce sama da masana’antun shinkafa 50 a jihar Kano aka rufe saboda karancin shinkafa a fadin kasa; Wasu manoma mata da miji ‘yan asalin Najeriya mazauna Amurka suna amfani da fasaharsu wajen inganta sana’arsu ta noma a jihar Maryland, da wasu rahotanni
Mataimakiyan sakatarin harkokin wajen Amurka mai kula da sha'anin Afrika Molly Phee ta bayyana cewa Ghana da Amurka za su ci gaba da hada hannu wajen tabbatar da mayar da dimokradiyya a Nijar.
Jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da jandarmomi sun dukufa da binciken motocin da ke fitowa daga ofishin jakadancin na Faransa da wadanda ke fitowa daga gidansa a Yamai.
Domin Kari