NIAMEY, NIGER - Kwanaki kadan bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023 ne Majalisar soja ta CNSP ta dauki matakin rufe sararin samaniyar kasar saboda abin da ta kira dalilan tsaro, lamarin da ya haddasa damuwa sosai a wajen jama’ar a ciki da wajen kasar.
Yanayin zaman dar-dar din da aka shiga a baya sakamakon barazanar CEDEAO game da harin da aka yi hasashen yiyuwar dakarunta za su kawo wa Nijar, ya sa Majalisar sojojin da suka kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum yanke shawarar rufe sararin samaniyar kasar a ranar 6 ga watan Agustan da ya gabata.
Amma bayan shafe makonni akalla hudu a karkashin wannan tsari, a sanarwar da suka bayar, hukumomi sun bayyana sake bude sararin samaniyar ga jiragen jigilar fasinja da na harakokin kasuwanci tsakanin Nijar da kasashen duniya, matakin da masanin sha’anin sufurin jirgin saman tsohon ma’aikacin filin jirgi Alhaji Moustapha Kadi ke ganin ya zo akan lokaci.
Sai dai jiragen sojoji da jiragen musamman ba za su ratsa sararin samaniyar Nijar ba sai da izini na musamman daga hukumomin kasar.
Shugaban kungiyar SIEN ta ‘yan kasuwar Import Export Alhaji Yacouba Dan Maradi na fatan ganin an zuba ido sosai kan jiragen da za su shigo da masu fita daga wannan kasa.
Matakin na zuwa a wani lokacin da ake fama da karancin man jirage sanadiyyar takunkumin ECOWAS, dalili kenan masana ke gargadin gwamnatin Nijar ta dauki wannan matsala da muhimmanci.
Sanarwar hukumomin ta ce an umurci ma’aikata su tashi tsaye kan na’urorin fake sararin samaniya don hango kai da kawon jiragen da za su ratsa kasar.
A yammcin Asabar din da ta gabata ne wa’adin ayyukan sojan Faransa a Nijar ya zo karshe kamar yadda hukumomin kasar suka shata, a yayin da a yau Litinin ake ci gaba da zaman dirshan a wuni na hudu a sansanin sojan Faransa da ke birnin Yamai a ci gaba da nuna matsin lambar ganin sun fice daga kasar.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna