Babbar kungiyar ‘yan adawar kasar Gabon, Alternance 2023, ta yi kira ga kasashen duniya a yau Juma'a da su karfafa wa gwamnatin mulkin da ta hambarar da shugaba Ali Bongo kwarin gwiwar ta mika mulki ga farar hula.
Gwamnatin mulkin sojan jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar soke dukkan wasu abubuwan alfarma ga koreren jakadan Faransa Sylvain Itte da iyalinsa sakamakon shudewar wa’adin da aka ba shi domin ya fice daga kasar.
Masu fashin baki a Najeriya sun yi kira ga gwamnatin kasar da dauki kwarararn matakai a sha'anin sako ruwa da ake yi daga madatsar ruwan Lagdo da ke kasar Kamaru, wanda ke haifar da mummunar illa a Najeriyar.
Shugabannin kasashen Afirka sun fara tattaunawa game da martanin da za su yi ga jami’an kasar Gabon da suka hambarar da shugaba Ali Bongo tare da nada nasu shugaban, wanda shi ne na baya bayan nan a jerin juyin mulki a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka da manyan kasashen yankin suka kasa magancewa
Wata mummunar gobara da ta tashi da daddare a wani gini mai hawa biyar a birnin Johannesburg da mutane marasa matsugunai ke zaune a ciki, ta kashe akalla mutane 73 da sanyin safiyar Alhamis, in ji ma’aikatan agajin gaggawa a babban birnin na kasar Afirka ta Kudu.
- 1960: 'Yancin Kai - Gabon ta samu 'yancin kai daga Faransa a ranar 17 ga Agusta, 1960, inda aka zabi Leon M'Ba a matsayin shugaban kasa a watan Fabrairu da ya biyo baya.
Al’umar kasar Gabon sun wayi gari da labarin juyin mulki Inda sojoji su ka hambarar da zababben shugaban kasa Ali Bongo wanda ya ya sake lashe zabe.
Yau laraba 30 ga watan Agusta ake bukukuwan tunawa da ranar mutanen da suka bata, wacce ta samo asali a 1983 da nufin karfafa gwiwa ga wadanda dangi ko makusantansu suka bace.
Faransa ta yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a Gabon, ta kuma yi kira da a mutunta sakamakon zaben kasar da aka gudanar a makon da ya gabata, kakakin gwamnatin kasar Olivier Veran ya fada a ranar Laraba 30 ga watan Agusta.
Ministocin tsaron kasashen nahiyar Tarayyar Turai za su tattauna halin da ake ciki a Gabon, in ji kungiyar EU.
Kowace shekara, ’yan kungiyar Zumunta suna haduwa a wuri guda domin sada zumunta da kuma duba yiwuwar yadda zasu taimaka wa juna da kuma yadda zasu bada nasu gudunmawa wajen cigaban Najeriya. Sannan yin hakan yana taimaka wa yaran da suke Haifa wajen fahimtar al’adu da mahimmancin hadin kai.
Matakin na zuwa ne sakamakon janye wasu ayyukan tallafawa 'yan cirani da kasashen suka yi bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yuli.
Gwamnatin Faransa ta tsayar da ranar hudu ga watan Satumba a matsayin ranar da dokar hana sanya Abaya a makarantun gwamnati za ta soma aiki a duk fadin kasar.
Wani rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a karshen makon jiya ya ayyana cewa kungiyar IS ta yi nasarar ninka hare-haren da take kai a kasar Mali sau biyu a tsawon shekara cikin shekara guda, abin da ke fayyace girman mamayar da kasar ta Mali ke fuskanta daga kungiyoyin ta’addanci.
Jakadan Faransa a Nijar zai ci gaba da zama a kasar duk da matsin lambar da shugabannin da suka yi juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli ke nunawa, a cewar hukumomin Faransa.
Yau 26 ga watan Augusta ake bikin Ranar Hausa ta Duniya, Hausawa mazauna Turai sun ci gaba da raya al’adunsu.
Domin Kari