Yau wata babbar kotun tarayyar Najeriya da ke zamanta a jihar Legas, ta bayar da belin wani dan kasuwa kuma mai ra’ayin jama’a, Pascal Okechukwu, wanda aka fi sani da Cubana Chief Priest, inda ta bukaci ya biya Naira miliyan 10, ya kuma gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa.