Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotun Amurka Ta Yanke Wa Wanda Ya Kafa Binance Hukuncin Daurin Watanni Hudu A Gidan Yari


Changpeng Zhao - Binance
Changpeng Zhao - Binance

A ranar Talata ne aka yanke wa Changpeng Zhao, tsohon shugaban kamfanin Binance, hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni hudu, bayan da ya amsa laifinsa na keta dokokin Amurka kan safarar kudade a babbar kasuwar hada-hadar kudi ta duniya.

WASHINGTON, D. C. - Zhao, mutumin da a da shi ne wanda aka ayyana a matsayin wanda mafi tasiri a masana'antar crypto, wanda kuma aka fi sani da "CZ," shine babban shugaban crypto na biyu da aka yanke masa hukuncin ɗaurin kurkuku.

Hukuncin da Alkalin Gundumar Amurka Richard Jones ya zartar a Seattle ya yi matukar gaza shekaru ukun da masu gabatar da kara ke nema, kuma kasa ne da matsakaicin shekaru 1 zuwa 1/2 da matakin tarayya ya ba da shawara a yanke.

Har ila yau, ya yi sauƙi fiye da shekaru 25 da Sam Bankman-Fried ya samu a cikin watan Maris saboda satar dala biliyan 8 daga abokan cinikanyarsa na FTX da yanzu ya kife. Bankman-Fried ya sake daukaka karar hukuncin da aka yanke masa.

Duk da haka, masu gabatar da kara sun yi murna da sakamakon binciken da aka kwashe tsawon shekaru ana yi kan Binance da Zhao, hamshakin attajirin da ya yi rayuwa nesa da Amurka a Hadaddiyar Daular Larabawa.

"Wannan wata babbar rana ce," in ji lauyan Amurka Tessa Gorman ga manema labarai a wajen kotun. "Daurin kurkuku yana da matukar muhimmanci a wannan shari'ar kuma mun gamsu da sakamakon."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG