Yayin da Trump da Biden za su sake karawa a zaben bana dukkansu sun tabo batun tashin hankalin 6 ga watan Janairun 2021 a yakin neman zabensu; Wasu manoma a jihar Neja dake arewacin Najeriya su na korafin cewa gwanmati ta kwace filayen su ne da karfi ba tare da diyya ba, da wasu rahotanni
'Yan sandan Kenya sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zanga da dama tare da toshe titunan hanyar zuwa fadar shugaban kasar a ranar Alhamis, yayin da ake ci gaba da gudanar da kananan zanga-zanga a garuruwa da dama.
A cewar rahotannin Majalisar Dinkin Duniya da dama, halin jin kai a Afganistan yana da muni. Fiye da kashi 50 cikin 100 na al'ummar kasar kimanın mutane miliyan 23.7 na bukatar agajin jin kai.
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa, Turkiyya na tsaye tsayin-daka da kasar Labanon a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun saka tsakaninta da Isra'ila, ya kuma yi kira ga kasashen yankin da su marawa Beirut baya.
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta samu wani shugaban masu tsattsauran ra'ayin Islama mai alaka da al-Qaida da laifin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a Timbuktu na kasar Mali.
Domin Kari