A watan Maris din da ya gabata, hukumomi suka rufe mahakar zinariya ci da karfi ta hillo dake kusa da kan iyakar Kenya da kasar Habasha biyo bayan asarar rayuka da dama sakamakon rikici tsakanin al’ummomi akan ikon shiga yankin, duk da haka mahakan sun cigaba da aiki a wurin.
A cewar mataimakin kwamishina mai kula da gundumar Marsabit, David Saruni, kimanin mutane 1000 ne suka mamaye yankin da yammacin Litinin din da ta gabata sakamakon fin karfin jami’an tsaron da suka yi.
“Sun haka wata mahakar da aka daina amfani da ita wacce ta rufta tare da hallaka mutane 5 din da aka zakulo gawawwakinsu, a cewar saruni a jiya Talata.
Wani dattijo a kauyen, Alio Guyo, ya bayyana cewar gawawwaki 9 aka zakulo daga karkashin baraguzai, da suka hada da ‘yan kenya 5 da ‘yan kasar habasha 4.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna