Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Shugaban Masu Safarar Miyagun Kwayoyi A Jihar Imo


NDLEA National Drug Law Enforcement Agency
NDLEA National Drug Law Enforcement Agency

Hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ta kama madugun safarar miyagun kwayoyin dake da hannu wajen sarrafawa tare da rarraba muguwar kwayar nan mai suna “methamphetamine", da ake kira da “mkpuru mmiri” a harshen Ibo.

NDLEA ta kama madugun fataken kwayar ne mai suna Joachim Mbono mai shekaru 42 da haihuwa bayan da ya gudo daga Afirka ta Kudu inda ya jima yana zaune, tare da koyo fasahar harhada kwayar ta methamphetamine, amma da aka fara gudanar da bincike akansa akan fataucin kwaya, sai ya dawo Najeriya tare da ci gaba da sana’arsa ta aikata laifin inda ya kafa dakunan gwaje-gwajen kimiya a kauyuka masu nisa domin boye miyagun ayyukansa.

Sanarwar da daraktan yada labaran NDLEA, Femi Babafemi ya fitar, a yau Talata, tace an kama Mbono da abokan sana’arsa a wani gida dake kauyen Umuomi, karkashin garin Uzogba Ezenomi, mai kwarya-kwaryar ‘yanci dake karamar hukumar Ikeduru ta jihar Imo.

Madugun dake da ofisoshi a jihohin Imo da Ribas ya shiga sahun wadanda NDLEA ke hako ne, bayan samun bayanan sirrin dake nuni da cewar yana da hannu wajen rarraba dimbin kwayar methamphetamine a yankin kudu maso gabashin Najeriya da kudu maso kudanci dama sauran sassan kasar.

Bayan shafe makonni ana bibiya, jami’an bangaren musamman na hukumar NDLEA suka bi diddigi tare da gano madugun a kasaitaccen gidansa dake kauyensu a jihar Imo, inda aka kama shi tare da wani mamba a kungiyarsa mai suna, Kenneth Ofeogbu mai shekaru 34, da adadin daban-daban na kwayar methamephetamine, da sinadaran da ake amfani dasu wajen hadata da bindiga kirar “pump action” da dimbin harsashai.

Kayayyakin da aka kwato daga gidan sun hada da fiye da gram 419 na kwayar ta meth, da gram 750 na iodine da gram 500 na sodium bicarbonate, wasu daga cikin sinadaran da ake amfani dasu wajen hada kwayar ta meth, da na’urar auna nauyi ta zamani da bindiga kirar “pump action” da kwanson harsashai 4.

Meth
Meth

Nan take jami’an NDLEA din suka mamaye wata maboyar Mbonu dake lamba 11 Redemption Avenue dake birnin Fatakwal na jihar Ribas, idan aka sake kwato karin kayayyakin da za’a gabatarwa kotu a matsayin shaida da suka hada da gram 750 na sarrafaffiyar hodar sodium bicarbonate da gram 170 na hodar da ba’a sarrafa ba da kuma gram 75 na kwayar ta meth.

Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa
Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa

A martaninsa, Shugaban Hukumar NDLEA ta kasa, Burgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin kamen mai sigogi da yawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG