Ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa a birnin Abidjan gari mafi girma a kasar Ivory Coast sun yi sanadin mutuwar mutane akalla 24 sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya na tsawon mako guda, kamar yadda hukumomi suka bayyana a yau Talata
Kusan gidajen mai 2,000 ne aka rufe a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya domin nuna adawa da shirin yaki da fasa kwaurin da hukumomi ke yi wa wasu dillalan man fetur.
'Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa da ruwa domin tarwatsa masu zanga-zanga a Nairobi babban birnin kasar Kenya da wasu biranen kasar a ranar Talata yayin da dubban mutane suka fantsama kan tituna a fadin kasar domin nuna adawa da shirin karin haraji
Gwamnatin jihar Ogun a Najeriya ta tabbatar da kamuwar mutane 25 da cutar kwalara a kananan hukumomi bakwai na jihar, yayin da mutum daya ya rasa ransa a karamar hukumar Ijebu ta Arewar jihar.
Yankin Dagestan da ke kudancin kasar Rasha ya gudanar da zaman makoki na kwanaki uku a yau Litinin bayan wani harin da mayakan Islama suka kai inda suka kashe mutane 19.
Wasu fashe-fashe sun yi sanadin tashin gobara a wata masana'anta ta batirin lithium a Koriya ta Kudu a ranar Litinin, inda suka kashe ma'aikata 22, mafi yawansu 'yan kasar China, yayin da kamfanin ya kone kurmus.
Irin gudunmuwar da wasu ‘yan gudun hijira ke bayarwa wajen kyautata rayuwar sauran mutane da ke zama a sansanonin; Bankin Duniya ya ce hada-hadar kasuwanci ta intanet ta na samar da hanyar karfafa tattalin arziki a fadin Najeriya tare da rage talauci, da wasu sauran rahotanni
A cewar rahoton masana a cibiyar Clingendael, kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin da aka yi ittifakin suna da alaka da al-qaeda suka rika tsallakowa daga yankin arewacin jamhuriyar Benin sun samu mafaka a gandun dajin gwamnati dake Kainji, daya daga cikin mafiya girma a Najeriya.
Ranar 20, ga watan Yuni na kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin duba halin da 'yan gudun hijira suke ciki a sassan duniya.
Domin Kari