Jama'a da dama a kudu maso gabashin Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu, game da hukuncin korar gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi da mataimakinsa Kelechi Igwe, wanda babbar kotun tarayya da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya ta yanke jiya Talata.
Akalla manyan kungiyoyin farar hula hudu ne suke cewa, yanzu sun shirya tsaf don gudanar da babban taron matasan Najeriya a jami'ar Nnamdi Azikiwe da ke Awka, babban birnin jihar Anambra, a yayin da zaben shekarar 2023 na gabatowa.
Jama'a da yawa da ma dillalan shanu a jihar Abia na ci gaba da yin tsokaci akan batun rufe babbar kasuwar shanu da mahautar garin Aba, da ke Najeriya da gwamnatin jihar ta yi.
Al’ummar Erei dai sun shafe shekaru suna takun saka a kan wani fili da rusassun yankin Gabashin kasar ya kafa kafin yakin basasar Najeriya a matsayin matsugunin na gonar ‘ya’yan manja.
Wasu masu ra'ayin Biafrar na kara tursasa wa al'ummar kudu maso gabashin Najeriya bin dokar zaman gida, tare da bankawa motoci da ababan hawa da ke tafiya wuta, da kuma lalata kayan sayarwa a duk inda suka tayar da shago a bude.
Kwanaki bayan kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biafra ta ayyana hana rera taken Najeriya da kuma hana cin naman shanu daga arewacin kasar a yankin Igbo.
A watan Yulin da ya gabata, IPOB ta ayyana umarnin zaman gida a kowacce ranar Litinin a jihar ta Anambra wanda ya fara aiki a watan Agusta.
Ohaeneze ta kuma yi kashedi ga ‘yan kungiyar ta IPOB kan dokar zama a gida da take kakabawa al’umar yankin.
Al'umomin garin Okigwe da ke jihar Imo da na garin Uturu a jihar Abia, na ci gaba da jimami da alhinin mutuwar Donald Edeh, wani dalibin makarantar Marist Comprehensive Academy da ke garin Uturu, da 'yan bindiga suka harbe har lahira a yammacin ranar Asabar.
Wasu 'yan asalin yankin kudu maso gabashin Najeriya na cewa tsoro ne ya sa akasarin al'ummar yankin ke ci gaba da zaman gida a kowace ranar Litinin, duk da cewar kungiyar IPOB mai fafutukar tabbatar da kasar Biafra da ta ba da umurnin, ta riga ta dakatar da wannan shirin.
Kungiyar kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo, ta yi karin haske game da kwamitin lauyoyin da ta kafa, don bin diddigi da kuma sa ido a shari'ar da ake yi wa Mazi Nnamdi Kanu, madugun kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra, yayin da zai ci gaba da gurfana a gaban kotu.
A farkon makon nan kungiyar ta IPOB ta yi yakuwar mambobinta ta kauracewa kayayyakin kasar na Kenya saboda rawar da ta zarge ta da taka wa wajen kama Nnamdi Kanu.
A ranar Talata Ministan shari’a Malami Abubakar ya bayyana cewa an cafke Kanu wanda yanzu haka yana tsare a ofishin jami’an DSS yana jiran shari’a.
Gwamnan jihar Imo Sanata Hope Uzodinma ya gana da shuwagabannin kungiyar manoma da masu fataucin albasa ta Najeriya a Owerri, babban birnin jihar jiya Alhamis.
Kungiyar kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo ta jaddada muhimmancin kasancewar 'yan kabilar a kasar Najeriya, tare da bada goyon baya ga nesanta kansu da gwamnonin kudu maso gabashin kasar suka yi daga ayyukan haramtacciyar kungiyar IPOB da ke fafutukar ballewa daga Najeriya.
Hukumomi a Jihar Imo, sun yi bayani game da kashe tsohon mai bai wa tsohon shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa Ahmed Ali Gulak, wanda wasu 'yan bindiga suka yi a safiyar jiya Lahadi.
Kungiyar matasa Fulani ta Jode Jam Fulani Youth Association of Najeriya, ta bayyana rashin amincewarta da matakin hana kiwo a fili da gwamnonin kudancin Najeriya suka ayyana a garin Asaba, babban birnin jihar Delta a kwanan nan.
Wasu dai na cewa dole ne a fuskanci yanayin fargaba a yankin kudu maso gabas saboda yadda tsaro ya tabarbare a tsawon watanni kalilan, wato daga watan Satumban bara zuwa yau.
Domin Kari