Wannan ya zo ne biyo bayan ficewarsu daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki.
A hukuncin da mai shari'a Inyang Ekwo ya bada, kotun ta jaddada cewa jimillar adadin kuri'u 393,042 da Dave Umahi ya samu nasara da su a zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris shekarar 2019 duk mallakar jam'iyyar PDP ne, kuma bisa ka'ida bai yiwuwa a kaurar wa jam'iyyar APC wadannan kuri'un.
Sabili da haka, kotun ta umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta yi maza ta amso sunayen 'yan PDP da zasu maye gurbin Dave Umahi da mataimakinsa, ko kuma ta sake gudanar da zaben gwamna a jihar Ebonyi, kamar yadda sashe 177 na kundin tsarin mulki na shekarar 1999 da aka gyara ya tanadar.
Wani lauya, Dakta Monday Ubani ya yi tsokaci game da wannan maudu'in, inda ya ke cewa, "Akan batun masu zartarwa, wato su gwamnoni da shugaban kasa, kundin tsarin mulki bai ce wani abu ba, kuma kundin tsarin mulki bai bayyana sauya sheka a matsayin daya daga cikin sharrudan cire gwamna ba," yayin da Comfort Eze tana mai cewa toh idan har haka ne abin, ya kamata majalisar alkalai ta fito sarai akan batun sauya sheka, don lamuran shari'a su dauki siffar da ya dace su dauka.”
Mista Obinna Dike wani mai sharhi ne kan lamuran yau da kullum, kuma ya ce sam bai dace ba ka lashe zabe da sunan wata jam'iyya, sannan ka fice wata jam'iyya kana mulki, saboda wadanda suka zabe ka da sunan jam'iyya ta farko ba wawaye bane.
Tuni jam'iyyar PDP ta mika sunayen Hon. Iduma Igariwey da Mr. Fred Udeogu a matsayin gwamna da mataimakin gwamna, yayin da Dave Umahi na nanata cewa yana nan daram a matsayin gwamnan jihar Ebonyi.
Yanzu bayanai na nuni da cewa al'ummar jihar Ebonyi na fama da wani yanayi na rudani saboda wannan al'amarin, amma kakakin rundunar 'yan sandan jihar Loveth Odah ta shaida cewa lamura na tafiya kamar yadda aka saba.
Tana mai cewa, "Ba abin da ke faruwa a jihar Ebonyi. Ebonyi na zaune lafiya kamar yadda ta saba."
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: