Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ohanaeze Ta Gargadi IPOB Kan Haramta Tutocin Najeriya A Yankinsu


'Yan Kungiyar IPOB masu Fafutukar Kafa Kasar Biafra.
'Yan Kungiyar IPOB masu Fafutukar Kafa Kasar Biafra.

Ohaeneze ta kuma yi kashedi ga ‘yan kungiyar ta IPOB kan dokar zama a gida da take kakabawa al’umar yankin.

Kungiyar kabilar Igbo ta Ohaneze ta Ndigbo ta ja kunnen kungiyar IPOB da ke fafutukar kafa kasar Biafra da ta guji haramta tutar Najeriya a kudu maso gabashin kasar.

Kungiyar ta kuma yi kashedi ga ‘yan kungiyar kan dokar zama a gida da take kakabawa al’umar yankin inda ta umarci jama’a su zauna a gida a ranar Asabar 1 ga watan Oktoba mai zuwa.

“Muna so mu gargadi kungiyar ta IPOB da ta daina wahalar da ‘yan kabilar Igbo, bai kamata a kirkiro wani yanayi na ta da hankali a yankin Igbo ba. Saboda sa matasa su cire tutar zai jefa su cikin hadari.” In ji Babban Sakataren kungiyar ta Ohaneze, Mazi Okechukcwu.

Okechukwu ya kara da cewa har yanzu yankin na kudu maso gabas na nan daram a cikin yankin tarayyar Najeriya.

Babban Sakataren ya kuma nesanta kungiyar da umarnin da kungiyar IPOB ke bayarwa.

A ranar Asabar din da ta gabata ne kungiyar ta IPOB ta raba wata sanarwa a birnin Awka da ke jihar Anambra inda ta umarci jama’a da su zauna a gida a ranar 1 ga watan na Oktoba.

Ta kuma ba da umarnin haramta saka tutar Najeriya a yankin na kudu maso gabashin na Najeriya.

A ranar 1 ga watan na Oktoba Najeriya za ta cika shekara 61 da samun ‘yancin kai.

Jama’a da dama a yankin kudu maso gabashin Najeriya na ta sukar matakin zaman gidan da kungiyar ta ce a yi, inda jama’a suka raja’a akan cewa ana jefa tattalin arzikin yankin cikin hadari.

Sai dai duk da haka, akwai wadanda suke goyon bayan matakin na IPOB wadanda kan yi korafin cewa zamansu a Najeriya ba ya amfanar su tare da goyon bayan haramta tutocin kasar a yankin.

Saurari cikakken rahoton Alphonsus Okorigwe:

XS
SM
MD
LG