Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Imo Uzodinma Ya Gana Da Kungiyar Manoma Da Masu Fataucin Albasa


Hope Uzodinma, Gwamnan Jihar Imo
Hope Uzodinma, Gwamnan Jihar Imo

Gwamnan jihar Imo Sanata Hope Uzodinma ya gana da shuwagabannin kungiyar manoma da masu fataucin albasa ta Najeriya a Owerri, babban birnin jihar jiya Alhamis.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumomi ke ci gaba da kara inganta dabaru da matsa kaimi wajen kawo karshen ayyukan 'yan awaren Biafra da ke gurgunta lamuran cinikayya da kasuwanci a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Alhaji Aliyu Isa shine shugaban kungiyar masu fataucin albasa ta Najeriya, kuma ya yi karin haske game da wannan ganawar. Ya ce a baya da suka yi yajin aiki, gwamnar ya neme su don jin dalilan da ya sa su ka daina kai albasa, inda suka gabatar mishi da bukatunsu wadanda suka hada da neman tsaro ga rayukarsu da dukiyokinsu, sannan a kafa kwamiti da ya kunshi mutanensu na yan arewa da mutanen kudun, daga karshe kuma a biya su asarar da aka yi musu

Gwamnatin jihar Imo ta bakin Alhaji Suleiman Ibrahin Suleiman, babban mai taimaka wa gwamnan jihar Imo na musamman kan lamuran arewaci ya ce gwamnan ya dau alkawarin daukan nauyin asarar da aka samu kuma zai biya kowa kudinshi, daga masu shanu har zuwa masu albasa.

Wannan na zuwa ne bayan wasu manyan 'yan kasuwa 'yan kabilar Igbo a karkashin jagorancin Cif Emmanuel Iwuanyanwu suka kira wani taro a Owerri, babban birnin jihar Imon ranar Laraban da ta gabata, inda suka bukaci 'yan Arewa masu harka a kudu maso gabas su lisafta asarorin da suka tabka sakamakon hare-haren 'yan awaren Biafra, tare da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin dukkanin mazaunan yankin.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

XS
SM
MD
LG