A hirar shi da Muryar Amurka, Mista Rwang Pam Jnr mai magana da yawun wadannan kungiyoyin ya bayyana shirin da kuma burin da ake nufin cimma.
Ya ce "Yayin da Najeriya ke da fiye da kashi 70 bisa dari na yawan matasa, ya dace a hada dasu a shugabanci. Tsarin da muke da shi a matsayinmu na kasa a yau, bai bada dama don shigar da matasa cikin tsarin tafiyad da lamura ba, kuma Najeriya ba za ta samu ci gaba mai dorewa ba, sai an shigo da matasa cikin tsarin shugabanci da kyau."
A nata bayanin, Augusta Nneka wadda aka dora wa alhakin kula da wannan taron, ta yi karin haske inda ta ce, "An tsara taron ne a matsayin taro mafi yawa na matasa masu sha'awar gina kasar Najeriya, musamman a yayin da zaben shekarar 2023 na karasowa da hanzari. Tunaninmu anan shine mu nuna muhimmancin ra'ayoyin matasa kan batutuwan da suka shafi gina kasar Najeriya. Kuma muna sa ran cewa wannan taron zai zama taro na mutanen da zasu jagoranci Najeriya nan gaba."
Augusta dai ta kara da cewa kimanin matasa dubu goma ne zasu halarci wannan taron a wannan watan Maris da ke zuwa, don tattauna yadda za a kara wa matasan kasar sha'awar shigan siyasa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: