Hukumar zaben Najeriya ta ce gayyaci kamfanoni don kera na'urar da ta dace da nufin komawa kada kuri'a nan gaba ta hanyar na'ura mai kwakwalwa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a jiya Lahadi cewa zai bukaci abokin takararsa na jam’iyar Demokrat a babban zaben uku ga watan Nuwamba, tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, da yayi gwajin kwayoyi kafin ko bayan muhawararsu ta ranar Talata.
Fiye da wata guda bayan babban bankin Najeriya CBN ya amince da fara aiki da tsarin bada lamanin da babu ruwa ga kananan da matsakaitan ‘yan kasuwa da sana’o’I, masu kula da lamura a wannan fanni na ci gaba da bayyana matakan da suka kamata a dauka da zai farfado da harkokin kasuwanci a kasar
An gudanar da taron karawa juna sani tare da tuntuba a jihar Borno inda ake fama da matsalar tsaro, yayin kiyaye ranar zaman lafiya ta duniya.
Hukumar tsaron kasar Uzbekistan ta ce an sami sake farfadowar ayyukan masu tsattsauran ra’ayin addini a kasar da ke tsakiyar Asiya, amma tarihin gwamnatin na fakewa da tsattsauran ra’ayin addini domin tunkarar ‘yan adawa ya sa masu lura da al’amura shakku akan lamarin.
A yau litinin Amurka za ta saka takunkumi akan mutane fiye da 24 da wadanda ke da hannu a shirin nukiliya da makamai masu linzami na Iran.
Yan bindings sun buwayi al'umma a Najeriya inda suka mamaye yankunan kasar da satar mutane domin neman kudin fansa.
Jamiyar APC a Najeriya ta zargi gwamnatin Jihar Zamfara da hada kai da jamian tsaro wajan kama mata magoya baya ana tsare wa
Akwai yuwuwar jihar Sakkwato a Najeriya nan gaba kadan zata zamo cibiyar hada-hadar ayukkan noman rani biyo bayan kokarin gwamnatin jihar na duba yuwuwar samarda madatsun ruwa a kananan hukumomi uku.
A kalla ‘yan kasar Belarus 100,000 ne suka mamaye titunan birnin kasar Minsk a jiya Lahadi, a wata zanga-zanga mafi girma ta kin jinin shugaba Alexander Lukashenko, bayan ya yi ikirarin samun nasara a zaben watan jiya da ake takaddama akai, da kuma abokan hamayyarsa suka ce yana cike da magudi.
Makwanni bakwai gabannin gudanar da zabe a Amurka, shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cewa ya yi abin a zo a gani wajen yaki da annobar coronavirus da kuma dakile yawan mace-mace a kasar.
Akalla kiristoci 270 sun kauracewa majami’un kasar Kamaru da suke ikirarin cewa basu yadda akwai COVID-19 ba. Wadanda suka kaurace din sun yi bayanin cewa sun ga wadanda suka bi sharudan da majami’u suka gindaya sun kamu kuma sun kumamutu da cutar.
Goyon baya da babban lauyan gwamnatin Amurka, Mai shari’a William Barr ke baiwa shugaba Donald Trump akan batun kiyaye doka da oda, da yake jadadawa a yakin neman zaben shugabancin kasa, ya haddasa muhawara akan rawar da ta dace ma’aikatarsa ta taka a harkarkokin siyasa.
Wani dan Najeriya ya yi yi kirarin cewa ya harhada maganin gargajiya da tsirai da ya hakikanta zai yi maganin cutar Korona sai dai jami'an lafiya sun ce babu tabbacin haka
Mazauna garin da Muryar Amurka ta yi hira da su sun bayyana cewa, i zuwa lokacin hirar, hukumomi basu riga sun isa inda lamarin ya faru ba, suka kuma ce gawarwakin ‘yan bangar suna daji ba ayi jana’izarsu ba.
Dubun dubatar masu zanga zanga 'yan kasar Belarus sun fito jiya Lahadi ranar zagayowar haihuwar Shugaban kasar suna bukatar ya sauka daga mulki.
‘Yan Sanda sun ce an harbe mutum daya ranar Asabar a birnin Portland dake jihar Oregon yayin da masu zanga zangar neman a mutunta rayukan bakaken fata suka karu a titunan kasar da masu goyon bayan shugaba Donald Trump.
Jiya Lahadi, hukumar shirya gasar La Liga ta kasar Spain ta sanar cewa kontiragin Lionel Messi na Barcelona na nan ya na aiki kwanaki bayan da ya bada sanarwa da ta bada mamaki cewa, yana so ya bar klob din ‘yan sa’oi bayan da ya ki zuwa a duba lafiyarshi gabanin kakar wasanni.
Domin Kari