Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun COVID-19 Yasa Ana Gujewa Wuraren Ibada a Kamaru


Shugaba Paul Biya
Shugaba Paul Biya

Akalla kiristoci 270 sun kauracewa majami’un kasar Kamaru da suke ikirarin cewa basu yadda akwai COVID-19 ba. Wadanda suka kaurace din sun yi bayanin cewa sun ga wadanda suka bi sharudan da majami’u suka gindaya sun kamu kuma sun kumamutu da cutar.

Daga cikinsu akwai ‘yar shekara 37, Annabella Tabot wadda ta ce ta bar majami’ar Tabemacles of Freedom saboda Fastonta ya rude ta cewa babu COVID-19. Tabot tace, Faston ya umurci mijinta dan shekaru 60 kada yaje asibiti maimakon haka ya dinga yi masa addu’a ya fitar mashi da aljanu.

“Lafiyarsa ta dinga tabarbarewa har ya mutu. Anyi sa’a gwamnati ta shigo ta killaceshi kuma sauran iyalinshi basu kamu ba.”

Gwamnatin Kamaru ta rufe majami’ar Tabemacles of Freedom a watan Agusta domin tana yin wa’azi cewa, COVID-19 maganar kanzon kurege ne. Da yawa daga cikin membobin majami’ar 300 sun bujirewa dokar gwamnati suka cigaba da yin ibada a wajen majami’ar.

Tun 5 ga watan Maris Kamaru ta sanar da sama da mutum dubu 19,000 suke dauke da COVID 19 kuma 415 suka mutu a cewa kididdigar Jami’ar Johns Hopkins.

Jihohin Kasar ta Afrika ta tsakiya sun dora alhakin kan halin ko-in- kula, da rashin ilimi da kuma gazawar wasu majami’u su ilimantar da masu ibada su fahinci hadarin dake tattare da COVID-19 daga cikin matsalolin da suka kara yawan masu cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG