Manufar wannan tsari na babban bankin ita ce karfafa gwiwar kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa da masu sana’o’in hannu domin su bada gudunmawar su ga yunkurin tada komadar tattalin arzikin Najeriya.
A karkashin tsarin, babban bankin Najeriyar zai rinka samar da kudaden lamani ga wannan rukuni na ‘yan kasuwa da wadanda ke gudanar da sana’o’in hannu, amma ta hannun bankunan kasuwanci dake tafiyar da harkokin su bisa tsarin bankin musulinci da babu ruwa a cikin sa.
Dr Sa’idu Ahmad Dukawa malami a Jami’ar Bayero ta Kano, dake Nazari a wannan fanni, ya yi tsokaci akan irin asarar da aka dade ana yi.
Yace “tsawon lokacin al’umma tana yin asara kuma gwamnati na yin asara a dalilin tsarin bankinmu. Al’ummar da take ta musulmi ce ta dage ba zata karbi bashi da ruwa ba. Saboda haka mutane da yawa ba sa cikin tsarin banki. To idan ko mutane da yawa ba sa cikin tsarin banki, gwamnati tana asara da yawa.Saboda haka yanzu riba ta zama biyu.”
Ya zuwa yanzu dai, bankuna uku zuwa hudu ne a Najeriya ke tafiyar da hada hadar kudade bisa tafarkin da babu ruwa a cikin sa.
Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari:
Facebook Forum