Rashin amincewar dan shekara 33, a duba lafiyarsa, ya tabbatar da niyar sa ta barin klob din da ya yiwa wasa iya rayuwarsa.
Messi wanda ya lashe lambar dan wasa mafi kwarewa a duniya har sau shida ya dage cewa kwontragin ya bashi daman barin klob din ba tare da biyan komai ba, abinda Barcelona ta musanta, yanzu kuma La Liga ma ta musanta hakan.
Hukumar Wasan na cewa zata amince ne kawai idan Agentina zata bada Euro miliyan 700 watau dalar Amurka miliyan $833million kafin ta kyale shi ya bar kulob din.
Domin biye ma wannan doka, hukumar La Liga ta ce ba zata amince da bukatar sallamar dan wasan dake wasa a karkashin hukumar wasan ta kasar Spain,ba har sai an biya kudin da sharadin kontaragin ya tanada, inji La Liga.
Wani hoton bidiyo daga kamfanin dillancin labaran Reuters, ya nuna ‘yan wasa suna dawowa daga gwajin coronavirus a jiya Lahadi amma ba a ga Messi ciki ba. Lokacin isa filin atisayi ya yi a daidai karfe goma na safiya, amma wata majiya a klob din ta tabbatar wa Reuters cewa Messi bai isa wurin ba.
Matsayan da La Liga ta dauka na zama kalubale ga Messi da kungiyar da ake sa ran zasu bashi wata sabuwar kwangila
Kungiyar Manchester City ta Firimiya lig ne da ake sa ran zata hada shi da tsohon kocin Barcelona Pep Guardiola, amma clob din mallakar Abu Dhabi ka iya shan fama wurin biyan euro miliyan 700 da kuma makudan albashin Messi.
Messi, wanda ya lashe kofuna sama da 30 a wasan sa klob din kasar Spain kana ya zura kwallaye sama da 600, yana daukar albashin kimanin euro miliyan guda a kowane mako.
Facebook Forum