Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Antoni Janar Barr Ya Kare Kansa A Kan Goyon Bayan Trump


Shugaba Donald Trump da Antoni Janar Barr
Shugaba Donald Trump da Antoni Janar Barr

Goyon baya da babban lauyan gwamnatin Amurka, Mai shari’a William Barr ke baiwa shugaba Donald Trump akan batun kiyaye doka da oda, da yake jadadawa a yakin neman zaben shugabancin kasa, ya haddasa muhawara akan rawar da ta dace ma’aikatarsa ta taka a harkarkokin siyasa.

Lokacin da Trump ya ziyarci Kenosha a jihar Wisconsin ranar talatar da ta gabata, domin ganewa idonsa barnar da aka yiwa cibiyoyin kasuwanci da kuma sanar da tallafi na gaggawa na dalar Amurka Miliyan 40, Trump ya tafi tare da Barr.

Da yake jaddada kalaman kampe din Trump a kan yadda mayaka suka mamaye zanga zangar da ake yi ta nuna kyama da nuna wariyar launin fata da zaluncin ‘yan sanda, Barr ya fadawa taron shugabannin al’umma, cewa bisa umurnin Trump ne ‘yan kwanaki da suka shige ya hada jami’an gwamnatin tarayya da zai tura Kenosha.

Birnin ya yi fama da mummunar zanga zanga biyo bayan harbin bakar fata ba Amurke Jacob Blake da jami’in dan sanda ya yi ranar 23 ga watan Agusta daya kashe masa barin jiki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG