Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zelenskyy Ya Garzaya Saudiyya Gabanin Tattaunawarsa Da Amurka


Yarima Mohammed Bin Salman na Saudi Arabiya lokacin sadawarsu da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy a Jeddah
Yarima Mohammed Bin Salman na Saudi Arabiya lokacin sadawarsu da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy a Jeddah

Amurka, wacce a da ita ce babbar kawar Ukraine, ta kara inganta manufofinta na lokacin yakin, a kokarinta na ganin an kawo karshen fada cikin gaggawa, tare da yin hulda kai tsaye da Moscow, da kuma katse taimakon soji da musayar bayanan sirri ga Kyiv.

Shugaban Ukraine Zelenskiy da Yarima Mohammed bin Salman a Riyadh
Shugaban Ukraine Zelenskiy da Yarima Mohammed bin Salman a Riyadh

Ana sa ran Zelenskyy zai gana da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya, wanda kasarsa ta taka rawa wajen shiga tsakani ta hanyoyi daban-daban tun bayan mamayar kasar Rasha a shekarar 2022, da suka hada da musayar fursunoni da daukar bakuncin tattaunawa tsakanin Rasha da Amurka a watan jiya.

UKRAINE/SAUDI-ARABIA
UKRAINE/SAUDI-ARABIA

Tattaunawar da za a yi ranar Talata tsakanin jami'an Amurka da na Ukraine, ganawar farko ce a hukumance tun bayan wata mummunar arangama da ta afku a zauren Oval Office na fadar White House tsakanin Zelenskyy da shugaban Amurka Donald Trump, ana kuma sa ran za ta mai da hankali kan yarjejeniyar ma'adinai da kuma yadda za a kawo karshen yakin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG